
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya kai ziyarar duba aikin gyaran da ake gudanarwa a babbar ma’ajiyar ruwan Goron Dutse, wadda ita ce cibiyar rarraba ruwa mafi muhimmanci da ke hidimtawa Kano Metropolis.
Dakta Hashim ya bayyana cewa ma’ajiyar tana da manyan tankuna uku masu ɗaukar ruwa lita miliyan 7.3, miliyan 11.2 da kuma miliyan 22.5, wanda gaba ɗaya ya kai lita miliyan 40.5.
Ya ce tankunan miliyan 7.3 da miliyan 11.2, waɗanda aka gina tun shekarar 1930, sun kasance a yashe sama da shekaru 30, yayin da kusan dukkan muhimman kayan aikin da ke wurin suka lalace sakamakon vandalisim.
A cewarsa, aikin gyaran na tafiya yadda ya kamata, inda ake sauya bututun ruwa a tankunan miliyan 7.3 da miliyan 11.2, yayin da ake ci gaba da aikin cire laka da datti (desilting) a tankin miliyan 22.5.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin shirye-shiryen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da su domin farfaɗo da samar da ruwa a faɗin jihar Kano.
Ya ƙara da cewa aikin gyaran ma’ajiyar Goron Dutse na gudana ne tare da sauran ayyukan da ake yi a cibiyoyin tace ruwa na Tamburawa da Challawa domin tabbatar da wadataccen ruwan sha ga al’ummar jihar.
Brown Pigeon News
