
Amurka ta sanar da ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare a Kudancin Iran, inda ta ce farmakin ya nufi wuraren harba makamai masu linzami da kuma wasu jiragen ruwa da ake zargin suna yunƙurin dasa nakiyoyi a yankin.
Cibiyar ayyukan sojin Amurka ta bayyana cewa an kai hare-haren ne domin kare dakarunta da muradun ƙasar daga barazanar da take fuskanta daga sojojin Iran, yayin da rikicin yankin ke ci gaba da ɗaukar sabon salo.
Kakakin cibiyar, Kyaftin Tim Hawkins, ya ce dakarun Amurka na ci gaba da ɗaukar matakan kariya tare da sanya ido kan duk wani motsi da zai iya haddasa sabon tashin hankali.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tsagaita wuta da rage zafin rikicin ta hanyar tattaunawa tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin Iran ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan hare-haren ba. Sai dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baqai, ya bayyana cewa an samu ci gaba a wasu sassan tattaunawar zaman lafiya, duk da cewa har yanzu ba a kai ga cimma yarjejeniya ta ƙarshe ba.
A nasa ɓangaren, Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya nuna fata cewa za a iya kaiwa ga matsaya mai dorewa bayan tattaunawar da aka gudanar tsakanin jami’an Iran da Firaministan Qatar.
Sabbin hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke ƙara nuna damuwa kan yiwuwar faɗaɗar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ka iya yin tasiri ga zaman lafiya da tattalin arzikin duniya baki ɗaya.
