
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Gombe domin fafatawa a zaɓen shekarar 2027.
An tabbatar da Pantami ne bayan kammala zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar ranar Talata a garin Gombe, inda masu ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyar suka amince da sunansa a matsayin wanda zai jagoranci PDP a zaɓen gwamnan jihar.
Shugaban Kwamitin Zaɓen fidda gwanin, Gregory Yenlong, ne ya bayyana Pantami a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yana mai cewa shi kaɗai ne ya tsaya takarar kujerar a ƙarƙashin jam’iyyar.
Yenlong ya ce an gudanar da tsarin cikin lumana da bin ƙa’idojin jam’iyya, tare da nuna cewa PDP na da yakinin cewa Pantami zai kawo gagarumin sauyi a siyasar jihar Gombe.
Masu goyon bayan Pantami sun bayyana farin cikinsu da nasarar, inda suka ce zaɓinsa alama ce ta haɗin kai da sabon fata ga jam’iyyar PDP a jihar.
Naɗin Pantami dai na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar jihar Gombe ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
