
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta sanar da cafke wasu mutane shida da ake zargi da hannu a laifukan satar shanu, hada baki wajen aikata laifi da kuma mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bassey Ewah ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sabon sashen yaki da manyan laifuka na VCRU a birnin Jos.
A cewarsa, rundunar ta samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Yahuza Sale bayan wani bidiyo da ya wallafa a shafin Facebook wanda ake zargin yana tayar da hankalin jama’a.
Sanarwar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin hada baki da wani mutum mai suna Victor Danladi, wanda aka fi sani da Boka, wajen aikata satar shanu ta hanyar amfani da bindigogin AK47 na gida.
Rundunar ta kara da cewa ta kwato bindigogi kirar AK47 na gida guda biyu tare da harsasai, baya ga wata karamar bindiga guda daya yayin gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamishinan ’yan sandan ya tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano karin bayanai da kuma cafke sauran wadanda ake zargi da hannu a lamarin.
Ya kara da cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa ga dokar kasa.
