Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara aiwatar da matakan tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
A zaman musamman da majalisar ta gudanar a ranar Alhamis, ta mika wa mataimakin gwamnan takardar sanarwar amsa tuhuma kan zarge-zargen da aka ce sun kai matsayin laifukan da za su iya haifar da tsige shi daga mukaminsa.
Sanarwar, wadda aka karanta a zauren majalisar yayin zaman, ta kunshi zarge-zargen rashin da’a mai tsanani, amfani da mukami ba daidai ba, da kuma saba wa amana ta jama’a.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Husaini, wanda ya yi wa manema labarai karin haske bayan kammala zaman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa shi ne ya gabatar da takardar tsige mataimakin gwamnan a gaban majalisar.
A cewarsa, mambobi 38 na majalisar ne suka sanya hannu kan takardar.
Ya kara da cewa bayan mika sanarwar, ana sa ran mataimakin gwamnan zai mayar da martani kan zarge-zargen cikin makonni biyu, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.
Ana sa ran karin bayani kan lamarin yayin da ake ci gaba da tafiyar da matakan.