
Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, kan alƙawarin da ya yi na sake buɗe iyakokin ƙasar idan aka zaɓe shi a zaɓen shekarar 2027.
Hadimin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce gwamnatin Tarayya ta riga ta buɗe iyakokin ƙasar tun ranar 14 ga watan Maris na shekarar 2024.
Dare ya ce abin mamaki shi ne yadda Atiku ke magana kan sake buɗe iyakokin ƙasar, alhali kuwa, a cewarsa, tuni gwamnati ta buɗe su.
Ya ƙara da cewa a ranar 14 ga watan Fabrairun 2026, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sake buɗe iyakar ƙasar da ke Kamba, a Jihar Kebbi.
Sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa hulɗar kasuwanci da zirga-zirga tsakanin Najeriya da ƙasashen makwabta.
Martanin Fadar Shugaban Ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da adawar siyasa ke ƙara zafafa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
A baya-bayan nan, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da alƙawarin Atiku na maido da tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta cire.
A ranar Juma’a kuma, Atiku ya sake bayyana aniyarsa ta sake buɗe iyakokin ƙasar da ya ce suna rufe, tare da yin alƙawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro cikin shekara guda idan har ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasar ta ce wasu daga cikin abubuwan da Atiku ke gabatarwa a matsayin manufofin da zai aiwatar idan ya samu nasara, tuni gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da su.
