
By Mutawakkilu Ibrahim Idris
An ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar marigayi Alhaji Adamu Dankabo a Jami’ar Bayero Kano (BUK), a wani taro da ya haɗa masana, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin girmama rayuwarsa da gudunmawar da ya bayar ga ci gaban al’umma.
Littafin, wanda marigayi Farfesa Balarabe Mai Kaba tare da Mustapha Muhammad da wasu marubuta suka rubuta, ya yi nazari mai zurfi kan rayuwar marigayin, tare da bayyana irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi, ci gaban tattalin arziki da ayyukan alheri a Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ba da muhimmanci ga adana tarihi da karrama mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa al’umma.

Ya bayyana marigayi Alhaji Adamu Dankabo a matsayin jagora mai hangen nesa, wanda rayuwarsa ta kasance abin koyi ga matasa da masu tasowa. Ya ƙara da cewa rubuta tarihin irin waɗannan mutane wata hanya ce ta tabbatar da cewa gudunmawarsu ba ta shuɗe ba.
Kwamishinan ya yabawa kwamitin shirya taron da marigayi Farfesa Balarabe Mai Kaba ya fara jagoranta bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa an taskace tarihin marigayin cikin littafi domin amfanin al’ummomin yanzu da na gaba.
Ya kuma ba da shawarar kafa gidauniya da sunan marigayi Alhaji Adamu Dankabo domin ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri, tallafa wa ilimi da kuma raya kyawawan manufofin da ya rayu a kansu.
A ƙarshen taron, Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da sayen kwafi 20 na littafin kan kuɗin Naira miliyan 20, a matsayin gudunmawa ga aikin wallafa littafin da kuma nuna goyon baya ga ƙoƙarin adana tarihi da karrama fitattun mutane da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban al’umma.
Matakin ya nuna aniyar gwamnatin jihar na ƙarfafa al’adar rubuta tarihi da kuma tabbatar da cewa gudunmawar fitattun ‘yan Kano na ci gaba da kasancewa abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.
