Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata laifuka da lalata amfanin gona a jihar.
Mutfwang ya bayyana cewa lokacin da ake kama masu laifi a Filato ana kai su Abuja ya wuce, yana mai cewa zai bai wa jami’an tsaro umarnin ɗaukar matakin gaggawa kan duk wanda aka samu yana lalata gonaki.

Gwamnan ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka, tare da bayyana cewa kashe mutum saboda sata ko mutuwar shanu babban rashin hankali ne, domin babu rai da za a kwatanta da dukiyar dabbobi.
Ya kuma buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton satar shanu ga hukumomi domin a nemo mafita ta doka maimakon ɗaukar fansa da kai hari.
