
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa wata mata wanda ya yi sanadin mutuwarta a yankin Maraban Jos a ranar 21 ga Yuni, 2026.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce wasu mutane sun fara kai wa matar hari ne bisa zargin cewa mai garkuwa da mutane ce.
Sanarwar ta bayyana cewa domin ceton rayuwarta, jami’an ‘yan sanda sun ceto matar tare da kai ta ofishinsu domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi mata.

Sai dai daga bisani, wasu fusatattun mutane sun kutsa cikin ofishin ‘yan sandan, inda suka farmaki jami’an tsaro tare da ƙwace matar daga hannunsu.
Rahotanni sun ce bayan an fitar da ita daga ofishin ‘yan sandan, mutanen sun kashe matar duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na kare ta.
Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta tabbatar da kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, tare da jaddada cewa bincike ya fara domin gurfanar da duk masu hannu a wannan aika-aika a gaban kotu.
Brown Pigeon News na ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da kawo muku ƙarin bayani yayin da bincike ke gudana.
