
Daga Brown Pigeon Media
Ministan Ƙaramin Harkokin Albarkatun Man Fetur (Gas), Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na kawo ƙarshen talaucin makamashi a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
Ekpo ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Ƙungiyar Masu Kula da Dokokin Man Fetur ta Afirka (AFRIPERF) ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Misis Oritsemeyiwa Eyesan, a hedikwatar NNPC da ke Abuja.
Ministan ya ce Najeriya na da damar jagorantar ƙasashen Afirka wajen inganta tsarin kula da harkokin makamashi, la’akari da yalwar albarkatun man fetur da iskar gas da kuma gogewar da ƙasar ta samu tsawon shekaru a fannin tsare-tsare da dokokin makamashi.
Ya kuma buƙaci AFRIPERF da ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tare da samar da manufofin da za su taimaka wajen amfani da albarkatun makamashin Afirka domin bunƙasa tattalin arziki cikin ɗorewa.
“Afrika ba za ta iya cimma cikakken ci gaban tattalin arziki ba yayin da miliyoyin al’ummarta ke fama da talaucin makamashi. Najeriya tana da matsayi na musamman wajen jagorantar wannan yunƙuri, musamman ta fuskar albarkatun iskar gas da kuma ƙwarewar da ta samu a fannin makamashi,” in ji Ekpo.
Ya tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ga duk wani yunƙuri da zai taimaka wajen magance matsalar makamashi a nahiyar.
Kano first

Tun da farko, shugabar AFRIPERF kuma Babbar Jami’ar Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC), Misis Oritsemeyiwa Eyesan, ta bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne domin haɗa hukumomin da ke kula da harkokin man fetur a Afirka tare da samar da dandalin tattauna matsaloli da manufofin bai ɗaya.
Ta ce daga cikin ayyukan AFRIPERF akwai daidaita dokokin kula da harkokin man fetur a nahiyar da kuma inganta amfani da kyawawan ƙa’idojin gudanarwa.
Eyesan ta ƙara da cewa ƙasashe da dama ciki har da Ghana, Somalia, Gambia, Madagascar, Sudan, Guinea da Togo sun nuna sha’awar shiga ƙungiyar, yayin da wasu ke kammala matakan amincewa a hukumance kafin su zama cikakkun mambobi.
#BrownPigeonMedia #EnergyPoverty #Nigeria #AFRIPERF #GasSector #AfricaDevelopment
