Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FEDERAL GOVERNMENT SUSPENDS PROPOSED WAEC, NECO REGISTRATION FEE HIKE

    July 13, 2026

    FG: FANNIN MA’ADANAI YA JAWO JARIN DALA BILIYAN 3 CIKIN SHEKARU UKU

    June 18, 2026

    GWAMNATIN TARRAYYA TA MUSANTA SHIRIN SOKE HUKUMAR NBAIS

    June 18, 2026

    DEMOCRACY DAY SPEECH: OUR GENERATION MUST SECURE PROSPERITY 

    June 12, 2026

    Senator Barau Reaffirms ECOWAS Parliament’s Commitment to Regional Unity at Commissioning of New ECOWAS Headquarters

    July 3, 2026

    DA DUMI-DUMI: Starmer ya yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

    June 22, 2026

    NETANYAHU YA SHA ALWASHIN HANA IRAN MALLAKAR MAKAMIN NUKILIYA

    June 13, 2026

    Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Hallaka Mutane a Philippines, Ana Fargabar Tsunami a Wasu Ƙasashe

    June 8, 2026

    THE COALITION OF YOUNG PATRIOTIC IMAMS OF JUMA’AT MOSQUES IN NORTHERN NIGERIA HONOURS WAIYA WITH “GWANI” TITLE

    October 4, 2026

    WAIYA YA HALARCI KHATAMAR SAUKAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA GUDA 3,313

    October 4, 2026

    52 Kano Residents Receive Free Urological Surgeries in Saudi-Supported Medical Outreach

    October 4, 2026

    NIGERIA: A NATION OF HOPE, STRENGTH AND POSSIBILITY

    October 4, 2026
  • Business

    KASEDA TA GUDANAR DA SHIRIN WAYAR DA KAI GA MSMEs KAN KA’IDOJIN NAFDAC A JIHAR KATSINA

    June 12, 2026

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026

    NewsNigeria’s Inflation Rate Climbs to 15.38% in March

    April 16, 2026
  • Education

    WAIYA URGES STUDENTS TO UPHOLD DISCIPLINE, PATRIOTISM AT INDEPENDENCE ANNIVERSARY

    October 2, 2026

    WAIYA COMPLETES PhD VIVA VOCE, EARNS NEW ACADEMIC DISTINCTION

    September 22, 2026

    Gov. Yusuf Reaffirms Education Priority, Commends Al-Istiqama University’s Impact

    September 19, 2026

    KANO RANKS FIRST IN EDUCATION SPENDING, SECOND IN CLIMATE GOVERNANCE

    September 13, 2026

    KANO GOVERNMENT INAUGURATES 14-MEMBER COMMITTEE TO OVERSEE HANDOVER OF SORTED RANO FACILITIES TO FEDERAL POLYTECHNIC

    September 11, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

    August 1, 2026

    Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

    June 19, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

    June 19, 2026

    SHAYAR DA NONON UWA ZALLA NA KARE YARA DAGA CUTUTTUKA — KWAMISHINAN LAFIYA

    June 16, 2026

    Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

    June 11, 2026
  • Politics

    WAIYA RECEIVES AHMAD S. ARUWA ON COURTESY VISIT

    September 29, 2026

    Dan Agundi Congratulates 21 New Kano Special Advisers, Urges Commitment to APC’s Success

    September 26, 2026

    KOTU TA SOKE TSAYAR DA PANTAMI A MATSAYIN ƊAN TAKARAR PDP A GOMBE

    September 24, 2026

    BARAU, ABBA AND THE NEW POLITICAL REALITY: WHY THE NOISE FROM SIDELINES WILL NOT DEFINE THEM.

    September 19, 2026

    𝟱𝟬 𝗠𝗔𝗝𝗢𝗥 𝗔𝗖𝗛𝗜𝗘𝗩𝗘𝗠𝗘𝗡𝗧𝗦 𝗢𝗙 𝗣𝗥𝗘𝗦𝗜𝗗𝗘𝗡𝗧 𝗕𝗢𝗟𝗔 𝗔𝗛𝗠𝗘𝗗 𝗧𝗜𝗡𝗨𝗕𝗨

    September 18, 2026
  • Sports

    Bichi First FC Unveils Abubakar Senior as New Technical Adviser

    September 11, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    If Super Eagles Fail to Qualify for World Cup, Nigerians Will Not Forgive Us – Ahmed Musa

    September 6, 2025

    Super Falcons striker and six-time African Women’s Footballer of the Year, Asisat Oshoala, has completed her move from Bay FC to Saudi Women’s Premier League side Al Hilal

    September 3, 2025
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka
Health

Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaJune 11, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link
Mutawakkilu Ibrahim Idris
Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka
Mutawakkilu Ibrahim Idris
Hukumar Kula da Asibitocin Kano Ta Tsaurara Matakai Kan Rashin Zuwa Aiki bisa Jadawalin Ayyuka

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano (HMB) ta bayyana cewa ba za ta lamunci rashin zuwa aiki, sakaci ko kuma karya jadawalin aiki (Shift da Call Duty) da aka amince da shi a dukkan asibitocin mataki na biyu da ke fadin jihar.

 

Sakataren Zartarwa na Hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ne ya bayyana hakan yayin wasu ziyarce-ziyarcen bazata da ya kai manyan asibitocin jihar domin tantance jajircewar ma’aikata wajen aiki, ingancin ayyukan kiwon lafiya da kuma yadda cibiyoyin ke gudanar da ayyukansu.

 

Dakta Nagoda ya nuna matukar damuwarsa kan yadda wasu ma’aikatan lafiya ke barin wuraren aikinsu duk da cewa suna cikin jadawalin masu aiki ko masu jiran kiran gaggawa, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin kwarewa, rashin da’a da kuma barazana ga rayukan marasa lafiya.

 

Ya ce, “Ba daidai ba ne ma’aikatan lafiya da aka dora wa alhakin ceton rayuka su rika barin wuraren aikinsu, Irin wannan hali na jefa marasa lafiya cikin hadari tare da rage amincewar jama’a da tsarin kiwon lafiyarmu.”

Kano first

 

Sakataren Zartarwan ya gargadi ma’aikatan cewa daga yanzu Hukumar za ta dauki tsauraran matakan ladabtarwa kan duk wanda aka samu da laifin karya jadawalin aiki. Ya ce duk wanda aka samu da laifi zai rasa alawus-alawus din da ya shafi aikin kira ko aikin lokaci, baya ga sauran hukuncin gudanarwa da dokokin aikin gwamnati suka tanada.

 

Dangane da bunkasa karin ma’aikata, Dakta Nagoda ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da kokarin kammala daukar karin kwararrun ma’aikatan lafiya domin cike gibin da ake da shi a asibitocin jihar. Sai dai ya bukaci shugabannin asibitoci da su yi amfani da ma’aikatan da ake da su cikin hikima da kwarewa wajen ingancin su har zuwa lokacin da za’a kammala daukar sabbin ma’aikatan.

 

Ya kuma bayyana cewa Hukumar ta kara karfafa tsarin sa ido da tantance ayyuka domin tallafawa kudirin gwamnati na inganta ayyukan kiwon lafiya da tabbatar da cewa al’umma suna samun kulawar lafiya mai inganci cikin sauki da kuma kan lokaci.

A wani mataki na tabbatar da da’a da rikon amana, an kuma bai wa wasu ma’aikatan da aka samu da laifuka yayin ziyarar takardun neman bayani wato (Query) nan take.

 

A matsayin wani bangare na inganta rikon amana da gudanar da aiki yadda ya kamata, Dakta Nagoda ya umarci dukkan shugabannin asibitoci da su tabbatar da manna sabbin jadawalin ayyukan yau da kullum a dukkan sassa da bangarorin asibitocin. Haka kuma ya jaddada muhimmancin tsafta da kula da muhalli a cibiyoyin lafiya domin samar da yanayi mai kyau ga marasa lafiya.

 

Tawagar binciken karkashin jagorancin Dakta Mansur Mudi Nagoda tare da daraktocin Hukumar ta ziyarci manyan cibiyoyin lafiya da suka hada da Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Asibitin Sheikh Jidda, Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa, Asibitin Waziri Gidado, Cibiyar Kula da Matsalolin mafitsara ta Abubakar Imam da Asibitin Mallam Ja’afar da sauransu.

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudirinta na gina tsarin kiwon lafiya mai inganci, mai saurin amsa bukatun jama’a kuma mai mayar da hankali kan marasa lafiya, inda kwarewa, sadaukarwa da rikon amana za su kasance ginshikan gudanar da ayyukan lafiya.

 

ZS/ RAM.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleGwamnatin Tarayya Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Talauci Ta Hanyar Kariyar Zamantakewa
Next Article NORTHERN YOUTH ASSEMBLY APPLAUDS NATIONAL ASSEMBLY’S HISTORIC PASSAGE OF STATE POLICE BILL

Related Posts

NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

August 1, 2026

Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

June 19, 2026

Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

June 19, 2026

SHAYAR DA NONON UWA ZALLA NA KARE YARA DAGA CUTUTTUKA — KWAMISHINAN LAFIYA

June 16, 2026

Race Against Time: KSCHMA Rapid Response Team Secures Emergency Surgery for Accident Victim at Sir Muhammad Sunusi Specialist Hospital

June 9, 2026

Zulum Sets 60-Day Deadline for 400-Bed Teaching Hospital, Orders Completion of Orthopaedic Hospital in Four Months

June 6, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

THE COALITION OF YOUNG PATRIOTIC IMAMS OF JUMA’AT MOSQUES IN NORTHERN NIGERIA HONOURS WAIYA WITH “GWANI” TITLE

By Brown Pigeon MediaOctober 4, 2026

The Coalition of Young Imams of Juma’at Mosques in Northern Nigeria (CYIJMNN) has honoured…

WAIYA YA HALARCI KHATAMAR SAUKAR ALƘUR’ANI MAI GIRMA GUDA 3,313

October 4, 2026

52 Kano Residents Receive Free Urological Surgeries in Saudi-Supported Medical Outreach

October 4, 2026

NIGERIA: A NATION OF HOPE, STRENGTH AND POSSIBILITY

October 4, 2026

WAIYA URGES STUDENTS TO UPHOLD DISCIPLINE, PATRIOTISM AT INDEPENDENCE ANNIVERSARY

October 2, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.