
jagoran jam’iyar NDC a kano , Rabiu Musa Kwankwaso ya bai wa Tijjani Gandu takarar kujerar majalisar jiha a ƙaramar hukumar Birni.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya zo ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a yankin domin tabbatar da haɗin kai da kuma ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓe mai zuwa.
Tijjani Gandu na daga cikin matasan siyasa da ke da tasiri a yankin Birni, inda magoya bayansa suka bayyana jin daɗinsu kan matakin da aka ɗauka.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa zaɓin Tijjani Gandu na nuna yadda jam’iyyar ke ci gaba da bai wa matasa dama a harkokin shugabanci.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar ba ta fitar da cikakken bayani kan shirye-shiryen yakin neman zaɓen ɗan takarar ba.
