
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta sanar da kama wasu ’yan ƙasar Mexico da ake zargi da hannu wajen sarrafawa da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Ogun.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri da suka kai su wani wuri da ake zargin ana gudanar da haramtaccen aikin, inda suka gano miyagun ƙwayoyi masu tarin yawa da darajarsu ta haura Naira biliyan 480.
A cewar hukumar, an kama mutanen ne tare da wasu kayayyaki da ake zargin ana amfani da su wajen sarrafa miyagun ƙwayoyin, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.
NDLEA ta bayyana cewa kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na dakile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma hana ayyukan da ke barazana ga lafiyar al’umma da tsaron ƙasa.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro na cikin gida da na ƙasashen waje wajen yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi da kungiyoyin da ke da alaƙa da irin waɗannan laifuka.
Wasu mazauna yankin sun yaba da matakin da jami’an tsaron suka ɗauka, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen rage yawaitar miyagun ƙwayoyi da illolin da suke haifarwa a cikin al’umma.
