
Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Rahotanni daga unguwar Kofar Mata a cikin birnin Kano sun bayyana cewa an samu tashin hankali bayan da wasu jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, wato National Drug Law Enforcement Agency, suka yi harbe-harbe yayin wani samame da suka kai yankin.
Shaidu sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an ke kokarin cafke wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, lamarin da ya haddasa rudani da firgici a tsakanin mazauna yankin da masu wucewa.
A cewar wasu ganau, harbe-harben sun jikkata mutane da dama ciki har da wata karamar yarinya da ake cewa harsashi ya same ta yayin da ake ta kokarin tserewa domin neman tsira.
“Mutane sun rude sosai saboda an fara jin karar bindiga ba tare da sanin abin da ke faruwa ba. Wasu sun fadi yayin gudu, wasu kuma sun samu raunuka,” in ji wani mazaunin yankin.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, yayin da iyalai da mazauna yankin ke nuna damuwa kan yadda harbe-harbe ke faruwa a wuraren da jama’a ke cunkushe.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumar National Drug Law Enforcement Agency ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da zargin da ake yi wa jami’anta kan lamarin.
Sai dai mazauna yankin sun bukaci hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano yadda al’amarin ya faru tare da daukar matakan da suka dace domin kare rayukan fararen hula.
