
Daga. Mutawakkilu Ibrahim
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
Mai Girma Gwamna,
Ina rubuto wannan wasiƙa ne domin jawo hankalinka kan yadda aka tsara kwamitin yaƙin neman zaɓenka, tare da bayyana wasu damuwa da nake ganin ya kamata a duba su cikin hikima da kulawa.
Mai Girma Gwamna, akwai alamun cewa ƙila ba a yi la’akari da wasu muhimman abubuwa ba wajen kafa wannan kwamiti. Akwai buƙatar a sake nazarin yadda aka zaɓi wasu daga cikin mambobinsa, domin tabbatar da cewa an zaɓe su ne bisa cancanta, ƙwarewa, amana da kuma jajircewa wajen gudanar da aikin da aka ɗora musu.
A ganina, wasu daga cikin waɗanda aka saka cikin kwamitin ba lallai ne sun samu wannan matsayi bisa cancantarsu ba. Akwai waɗanda ake ganin an saka su ne saboda wasu dalilai na daban, alhali kuma wasu daga cikinsu ba su da isasshen lokacin da za su sadaukar wajen yi maka hidima da gudanar da ayyukan da aka ɗora musu.
Haka kuma, akwai wasu mambobin da su kansu suke da burin tsayawa takara, don haka suna da nasu ayyuka da manufofin siyasa da za su iya ɗaukar lokacinsu. Wannan na iya rage lokacin da ya kamata su ware domin gudanar da ayyukan kwamitin yadda ya dace.
Mai Girma Gwamna, ya kamata a fahimci cewa nasarar kowace tafiya ta siyasa tana buƙatar mutane masu kishin tafiyar, masu gaskiya, masu jajircewa, waɗanda za su ba da lokacinsu da ƙarfinsu domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Saboda haka, ina ganin zai dace a sake duba tsarin wannan kwamiti, a tantance gudummawar da kowane mamba zai iya bayarwa, tare da tabbatar da cewa an bai wa waɗanda suka cancanta damar yin aiki bisa ƙwarewarsu da jajircewarsu.
Wannan shawara ba don sukar kowa ba ce, sai dai domin a ƙarfafa tafiyar siyasa, a gyara inda ake ganin akwai gibi, kuma a tabbatar da cewa duk wanda aka ba nauyin aiki ya kasance mai iya sauke wannan nauyi.
A ƙarshe, Mai Girma Gwamna, ina fatan za a ɗauki wannan saƙo a matsayin shawara ta gaskiya da nufin ganin an inganta tsarin tafiyar, an yi amfani da mutanen da suka dace, kuma an cimma manufofin da aka sa a gaba.
Allah Ya taimaki Jihar Kano, Ya ba ka ikon sauke nauyin da ke kanka, Ya kuma ba ka nasarar gudanar da ayyukanka cikin adalci da hikima.
