
Kungiyar kansiloli ta TUNUBU ABBA GRASSROOTS COUNSELORS FORUM a Jihar Kano ta gudanar da gagarumin saukar Alƙur’ani mai girma da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah da nasarar sake zaɓen Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a babban zaɓen shekarar 2027.
An gudanar da taron ne karkashin jagoranci da goyon bayan Mai Girma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya yaba wa kungiyar bisa wannan yunƙuri na haɗa malamai da jama’a domin yi wa Jihar Kano addu’ar zaman lafiya da ci gaba.
Taron ya samu halartar fitattun malaman addinin Musulunci da mahaddatan Alƙur’ani, inda aka gudanar da karatun Alƙur’ani mai girma tare da gabatar da addu’o’i na musamman.
Daga cikin manyan malaman da suka halarci taron akwai Sarkin Malaman Dorayi, Malam Sani Tilo, Malam Dauda Lokon Makera, da sauran malamai da mahaddatan Alƙur’ani.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar, Hon. Kabiru Maraska, ya bayyana cewa kungiyar ta kuduri aniyar yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a babban zaɓen shekarar 2027.
Hon. Maraska ya ce kansilolin da ke ƙarƙashin wannan dandali za su ci gaba da aiki kafada da kafada wajen ƙarfafa tushen goyon bayan gwamnati daga matakin ƙasa, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin ci gaba da ayyukan da gwamnatin jihar ke gudanarwa.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yaba wa shugabanni da mambobin kungiyar bisa shirya wannan taro na saukar Alƙur’ani da addu’o’i.
Waiya ya jaddada cewa addu’a na daga cikin manyan hanyoyin neman taimakon Allah, musamman a lokutan da ake buƙatar zaman lafiya, haɗin kai da nasarar ayyukan al’umma.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati tana sane da irin ayyukan wasu masu ƙoƙarin kawo rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnati da jama’a, yana mai cewa lokaci yana ƙara ƙaratowa da za a fara bayyana masu irin wannan hali a fagen siyasa.
Kwamishinan ya buƙaci magoya bayan gwamnati da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri da jajircewa, tare da mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kai da kare muradun Jihar Kano.
Ya ce haɗin kai tsakanin shugabanni, kansiloli, malamai da sauran al’umma shi ne ginshiƙin samun nasara da dorewar ci gaba.
A ƙarshen taron, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya amsa addu’o’in da aka gabatar, Ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano, tare da bai wa shugabannin jihar ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alheri domin amfanin al’umma.
