
Kwamishinan yada labarai da Al’ amurran cikin gida na jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan yayin rufe bitar kwanaki biyar da gidan radion ta shirya wa ma’aikatan sashin labarai da al’amurran yau da kullum na gidan radion jihar Kano, musamman masu tace labarai da masu dauko rahoto wanda aka gudanar a ƙaramin ɗakin taro na gidan rediyon.

Kwamared Ibrahim Abdullahi wayya yace suna sa ido akan yadda ake ake tafiyar da al’amuran radiyon kasancewarta ta na karkashin ma’aikatar yada labarai tare da bada tabbacin bunkasa ayyukanta da sauran al’amuran gidan radion.
Tun da farko da ke jawabi shugaban gidan rediyon Kano kwamared Abubakar Adamu Rano yace sun shirya horan ne domin zamanantar da aikin jarida domin yayi dai dai halin da ake ciki a yanzu.
Ya kara da cewa masu dakko rahoto hamsin da biyu da masu tace labarai 22 ne suka karbi horon.
Ya Kuma jaddada cewa zasu cigaba da horas da ma’aikatan gidan rediyan Wanda hakan yayi dai dai da kudirin gwamnatin jihar Kano na bunkasa tsarin ayyukan gwamnati da ma,aikata.
Taron ya Sami halattar daraktocin gidan da tsohon Daraktan shirye-shirye na AM da shugabanni da daraktoci na sashi daban-daban na gidan radion kano
