
Kamfanin mai na kasa NNPCL ya fara shirin sallamar kaso 70 na ma’aikatansa da wa’adin kammala aikinsu ya kusa karewa bisa radin kansu.
Shirin da aka yiwa lakabi da “Accelerated Exit Scheme AES” ya shafi ma’aikatan da suka ragewa shekara daya su yi ritaya a 2026, da wani mai lakabin “Voluntary Exit Scheme VES” wanda zai baiwa wadanda za su kammala aiki a shekarar 2027 zuwa 2030 damar ajiye aiki bisa radin kansu.
Kano first

Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin Bashir Ojulari ya ce wannan wani bangare ne na sauya fasalin kamfanin domin kara inganci da ba da dama ga matasa kwarru.
Ya jaddada cewa shirin ba na tilastawa ba ne, kuma ma’aikatan da suka yi ritaya da wuri za su samu kyauta mai yawa fiye da jira har shekaru 60.
Jami’ai sun ce shirin zai rage nauyin albashi, da bude hanya ga sababbin ma’aikata fiye da Dubu Daya da aka dauka bara, sannan ya zuba sababbin kwararru masu fasaha a kamfanin a yayin da aka sauya shi zuwa kamfani mai zaman kansa karkashin dokar PIA.
