
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu kuri’u dubu biyar da ɗari biyu da saba’in da bakwai (5,277) a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ƙaramar hukumar Gwale da ke jihar Kano, yayin da abokin takararsa, Stanley Osifo, bai samu ko kuri’a guda ba.
Zaɓen wanda aka gudanar cikin yanayi na lumana ya gudana ne a tsarin “ƙato bayan ƙato”, inda wakilai da masu ruwa da tsaki suka fito domin bayyana goyon bayansu ga shugaban ƙasar domin sake tsayawa takara.
Abin da ya ja hankalin jama’a shi ne yadda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci karɓar sakamakon zaɓen a matsayin wakilin shugaban ƙasa.
Da yake jawabi bayan bayyana sakamakon zaɓen, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya karɓi sakamakon cikin gamsuwa, tare da bayyana fatan cewa al’ummar jihar Kano za su ci gaba da bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya domin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar jama’a a birane da karkara.
Gwamna ya kuma bayyana cewa har yanzu wasu daga cikin al’ummar Kano ba su fahimci manufofi da irin jagorancin Shugaba Tinubu ba, wanda a cewarsa ne ke haddasa yawan mummunar fahimta da ake yi masa a tsakanin wasu jama’a.
A nasa ɓangaren, wakilin ɗan takarar Stanley Osifo, Alhaji Ishaq Ibrahim Muhammad, ya ce sun amince da sakamakon zaɓen cikin kwanciyar hankali, tare da yi wa abokin takararsu fatan alheri a matakai na gaba.
