
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda gwamnonin ƙasar suka gudanar da shirye-shirye tare da tafiyar da zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar APC a faɗin jihohin Najeriya.
Da yake jawabi a mazaɓarsa da ke Ikoyi bayan kammala kaɗa ƙur’arsa, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓukan suka gudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yadda aka tsara.
“Wannan ita ce siyasa ta gaskiya, siyasa daga tushe, inda kowane mamba na jam’iyyarmu ke da damar shiga zaɓe kamar yadda ni ma na fito na yi,” in ji shugaban ƙasar.
Shugaban ya bayyana cewa tsarin zaɓen ya nuna irin ƙarfafa dimokraɗiyya da jam’iyyar ke yi tare da bai wa mambobinta damar bayyana ra’ayoyinsu cikin ’yanci.
Tinubu ya ƙara da cewa yadda aka gudanar da tarukan jam’iyya tun daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi da kuma tantance ’yan takara ya nuna jajircewar shugabannin jam’iyyar wajen tabbatar da adalci da bin doka.
“Haƙiƙa na gamsu da yadda gwamnoni suka yi ƙoƙari a jihohinsu wajen shirya tarukan jam’iyya da zaɓukan fidda gwani cikin nasara,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da haɗin kai domin ƙarfafa dimokraɗiyya da ci gaban ƙasa.
