
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya halarci gagarumin taron khatamar saukar Alƙur’ani Mai Girma guda 3,313, tare da ƙaddamar da sabon suna na Ƙungiyar Matasan Limaman Jumu’a Masu Kishin Arewacin Najeriya.
An gudanar da taron ne domin yin addu’a da neman albarka ga ƙasar Najeriya, Jihar Kano da kuma shugabanninta, tare da jaddada muhimmancin Alƙur’ani Mai Girma wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da kyakkyawar tarbiyya a cikin al’umma.
A yayin taron, an gudanar da addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, ci gaba da wadata ga Najeriya da al’ummarta, musamman Jihar Kano.
Haka kuma, taron ya kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin matasa da malaman addini, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da yaɗa saƙonnin zaman lafiya, ɗa’a da kishin ƙasa.
An roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya sanya Alƙur’ani Mai Girma ya zama haske, shiriya da ceto ga mahalarta da al’ummar Musulmi baki ɗaya, Ya kuma albarkaci Najeriya, Jihar Kano da shugabanninta.
An kammala taron da addu’o’i na musamman ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
