
Sabon Jakadan Tarayyar Turai (EU) zuwa Najeriya da ECOWAS, Mai Girma Pedro Savaira, ya kai ziyarar aiki zuwa Kano, wadda ta kasance ziyara ta farko a hukumance a wajen Abuja tun bayan fara aikinsa.
Jakadan ya ce ziyarar tasa ba ta tsaya ga gaisuwar ban girma ba, sai dai domin fahimtar Kano, al’ummarta, hukumominta da kuma dimbin damar da jihar ke da su.
A ganawar da ya yi da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, sun tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin EU da Gwamnatin Kano a fannonin siyasa, yaɗa labarai da sadarwa.
Haka kuma, an duba damar haɗin gwiwa a ilimi, kiwon lafiya, noma, makamashi, matasa da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire, tare da ƙara hulɗa da al’ummar masu magana da Hausa.
Kwamishinan Waiya ya kuma gabatar da wasu muhimman ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ciki har da Safe Corridor Programme, wanda aka ƙaddamar domin yaƙi da daba da tashe-tashen hankulan siyasa ta hanyar gyara, ƙarfafawa da mayar da matasa cikin al’umma.
Waiya ya ce gwamnatin Kano a shirye take ta yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki domin ci gaban jihar.
“Ci gaban Kano ya fi girman bambancin ra’ayin siyasa.”
Ya ce Kano a buɗe take ga haɗin gwiwa, sabbin dabaru da damarmaki da za su inganta rayuwar al’ummarta.
Brown Pigeon News | Labarai Cikin Gaskiya da Sahihanci
