
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki kasa da ke neman kafa rundunar ‘yansandan jihohi a ƙasar.
Sanatoci sun amince da kudirin ne a ranar Laraba bayan nazari da amincewa da sashi na 26 na kudirin dokar a zaman kwamitin majalissar kan gyaran kudirin dokar
Kudirin na da nufin samar da doka da zata bai wa jihohi damar kafawa da gudanar da rundunonin ‘yansandansu tare da ci gaba da wanzuwar rundunar ‘yansandan tarayya.

Amincewa da kudirin gyaran dokar na ɗaya daga cikin manyan matakan da ake ɗauka domin sauya tsarin tsaro a ƙasar, yayin da ake sa ran a kammala sauran matakan dokar Kafin ta fara aiki a hukumance
