
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shidan farko na haihuwa.
Abubakar labaran ya bayyana haka yayin da yake jawabi kan alfanun shayar da jarirai nonon uwa, inda ya ce hakan zai taimaka wajen kare lafiyar yaran da inganta ci gaban kwakwalwarsu da kuma rage kamuwa da cutuka.
Kano first

Ya kara da cewa daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da matsalar karancin basira da rashin ingantaccen ci gaba a tsakanin wasu yara na da nasaba da rashin ba su nonon uwa yadda ya kamata tun daga haihuwa
Dakta Abubakar Labaran ya bukaci iyaye mata da su rungumi wannan dabi’a domin tabbatar da lafiyar ‘ya’yansu da kuma gina lafiyayyar al’umma