
Daga Mohammed Babagana Abubakar
Coordinator, Unifier Project – Jihar Kano
A kokarin da ake yi na gina kasa mai dorewa, wani hoto da ya bayyana na Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, ya wuce matsayin hoto na al’ada. Wannan hoto na dauke da sako mai zurfi na hadin gwiwa, wanda ke nuna sabuwar alkiblar da tattalin arzikin kasa ke fuskanta inda hadin kai ya zama jigon cigaba.
Hadin Gwiwa. Tubalin Ci Gaba Mai Dorewa
Shirin “Energize” ya fito a matsayin muhimmin ginshiki a karkashin tafiyar maigirma gobna Abba Kabir yusuf, wanda ke da nufin tabbatar da daidaito da kyakkyawar alaka tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Jiha. Wannan hadin gwiwa na nuni da cewa, idan ana maganar inganta rayuwar talakawa da bunkasa kasuwanci, muradun cigaban kasa sun fi duk wani bambancin siyasa karfi.
Taken shirin, “Commercialization Now” (Maida Kasuwanci zuwa Tsari na Zamani Yanzu), wani muhimmin kira ne ga al’umma musamman a Jihar Kano, cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya. Shirin na da manyan manufofi kamar haka:
Sauya kananan sana’o’in karkara zuwa ingantattun masana’antu masu tasiri.
Amfani da makamashi (musamman lantarki da hasken rana) domin tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tsaiko ba.
Bunkasa damar mata da matasa ta hanyar samar da jari, horo, da fasahar zamani.
Tasirin Shirin ga Jihar Kano
A matsayinta na cibiyar kasuwanci, Jihar Kano na da dimbin ‘yan kasuwa kanana a matakin mazabu da gundumomi. A karkashin shirin “Energize”, ana sa ran samun gagarumin sauyi kamar haka:
Inganta samar da wutar lantarki da makamashin hasken rana ga kananan masana’antu.
Kyautata hanyoyin sufuri domin saukaka kai kayan amfanin gona zuwa manyan kasuwanni cikin sauki.
Karfafa tattalin arzikin mata ta hanyar shirye shiryen gidauniyar Uwargidan Shugaban Kasa (RHI), musamman a yankunan karkara.
A yau, abin da ake bukata shi ne cikakken goyon baya daga al’umma. Muna kira ga membobin Unifier Project da daukacin jama’ar Jihar Kano da su rungumi wannan shiri domin cin gajiyar damar da yake dauke da ita.
Hadin gwiwar da ke tsakanin Abba Kabir Yusuf da Oluremi Tinubu ya nuna cewa akwai kyakkyawar makoma idan aka hada karfi da karfe.
Burinmu shi ne ganin kowane lungu da sako na Jihar Kano ya amfana da wannan sabon makamashi na cigaba.
Tare muke domin hadin kai, tare kuma za mu cimma cigaba.
