
Daga Abdu Saidu
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano, Hon. Suraj Ibrahim Imam, ya gudanar da addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da ingantaccen shugabanci a Dala, Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, ya yin da ya cika shekara biyu a kan karagar mulki.
An gudanar da addu’o’in ne a ranar Asabar a sakatariyar ƙaramar hukumar, inda kusan mahaddata Alƙur’ani guda 60 daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar suka halarci taron domin karatun Alƙur’ani mai girma.
Mahalarta taron sun kuma yi addu’o’in neman nasara ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta Jihar Kano, da sauran shugabannin siyasa.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Imam ya bayyana cewa an shirya addu’o’in ne domin gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa damar da ya ba shi ta jagorantar al’ummar Dala tsawon shekaru biyu, tare da neman ƙarin nasara, albarka da taimakonsa ga ƙaramar hukumar Dala, jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa taron ya kuma kasance wata dama ta roƙon Allah ya ba Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran shugabannin siyasa nasara a harkokin jagoranci da ayyukansu na siyasa a nan gaba.
Dangane da nasarorin shugabancinsa, ya bayyana cewa an gudanar da ayyukan raya ƙasa da dama a faɗin unguwanni 12 na ƙaramar hukumar cikin shekaru biyu da suka gabata, tare da goyon baya da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Sannan kuma ya yaba wa gwamnan bisa ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen ci gaba da yake aiwatarwa a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar, musamman a fannonin kiwon lafiya, ilimi, tsaro, gine-ginen hanyoyi, samar da ruwan sha, noma da samar da ayyukan yi.
A cewarsa, waɗannan ayyuka da tsare-tsare sun taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da bunƙasa ayyukan ci gaba a matakin ƙananan hukumomi.
Hon. Imam ya bayyana kwarin gwiwarsa ga jagorancin gwamnan, tare da kira ga mazauna ƙaramar hukumar da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su mara masa baya a zaɓen shekarar 2027. Haka kuma, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Taron ya samu halartar Alhaji Bashir Ibrahim Al-Mustapha, OON, kansiloli, mahaddata Alƙur’ani, masu ba da shawara kan harkokin siyasa, sakataren ƙaramar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Ƙaramar Hukumar Dala.
