
Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar, Dr. Dahir Muhammad Hashim, ta gudanar da aikin tsaftace muhalli na ƙarshen wata, domin ƙarfafa tsaftar muhalli da kare lafiyar al’umma.
A yayin gudanar da aikin, Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Hadi Bala Yahaya, MNI, ya jagoranci tawagar jami’an Ma’aikatar wajen gudanar da ziyarar duba tsaftar muhalli a wasu manyan asibitoci a Jihar Kano.
Asibitocin da aka ziyarta sun haɗa da Asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase, Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da kuma Asibitin Sir Muhammadu Sunusi.
A yayin ziyarar, tawagar ta duba yanayin tsaftar muhallin asibitocin da kuma yadda ake gudanar da ayyukan kula da muhalli domin kare lafiyar marasa lafiya, ma’aikatan lafiya da sauran masu ziyartar asibitocin.
Bisa bayanan da aka samu yayin ziyarar, asibitocin da aka ziyarta sun nuna kyakkyawan yanayin tsaftar muhalli tare da ƙoƙarin tabbatar da kiyaye tsafta a muhallinsu.
Ma’aikatar ta jaddada muhimmancin ci gaba da kula da tsaftar wuraren jinya, bandakuna, magudanan ruwa da wuraren zubar da shara, tare da tabbatar da cewa ana sarrafa sharar asibiti yadda ya kamata domin rage haɗarin yaɗuwar cututtuka da kare lafiyar jama’a.
Haka kuma, Ma’aikatar ta yi kira ga al’umma da hukumomi masu ruwa da tsaki da su ba da haɗin kai wajen kiyaye tsaftar muhalli, guje wa zubar da shara a wuraren da ba su dace ba, tare da kare magudanan ruwa daga toshewa.
Ma’aikatar ta ƙara jaddada cewa tsaftar muhalli nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ba gwamnati kaɗai ba, don haka wajibi ne kowane ɗan ƙasa ya taka rawar gani wajen tabbatar da tsaftar muhallinsa.
Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin Ma’aikatar na ƙarfafa wayar da kan jama’a da inganta tsaftar muhalli, domin samar da muhalli mai kyau, tsafta da aminci ga lafiyar al’umma a faɗin Jihar Kano.
SAHANNU:
BARA’ATU ALI BUNAWA
Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano.
