
Idan kishin Kano shi ne abin da muka sanya a gaba, to dole ne mu duba abin da zai amfani jihar Kano, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko jam’iyya ba. Kano na bukatar shugabanci mai hangen nesa, jajircewa da kuma kishin al’umma.
A yau, idan mutum ya yi tafiyar kilomita guda kacal a cikin wasu sassan jihar Kano, akwai yiwuwar ya ci karo da wani aiki ko wani shiri da gwamnatin Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ta aiwatar ko ta fara aiwatarwa. Wannan shi ne abin da ya sa muke cewa aikin gwamnati ba magana ce kawai ba; aiki ne da ake iya gani a zahiri.
Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa jagoranci ba wai zama a ofis kawai ba ne. Jagoranci shi ne fita cikin al’umma, fahimtar bukatun jama’a da kuma mayar da su manufofin gwamnati masu amfani.
Daga ayyukan raya ababen more rayuwa zuwa bangaren ilimi, lafiya, muhalli da sauran fannoni, akwai abubuwan da suka nuna cewa gwamnati na kokarin sauke nauyin da aka dora mata.
Abu ne mai wahala ka yi tafiyar kilomita ɗaya a Kano ba tare da ganin wani sauyi ko wani aiki da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo ba. Wannan ba wai yabo kawai ba ne; kira ne ga jama’ar Kano da su duba abin da ke faruwa da idonsu.
A siyasa, lokaci zuwa lokaci jama’a kan samu damar tantance wanda ya yi alkawari da wanda ya fara cika alkawari. A ganina, wannan shi ne lokacin da ya dace mu fifita kishin Kano da ci gaban al’ummarta sama da duk wata sabani ta siyasa.
Abba Kabir Yusuf ya cancanci a duba tarihin aikinsa, ba kawai kalamansa ba. Idan aiki ne ake amfani da shi wajen auna shugabanci, to akwai hujjoji da dama da ya kamata jama’ar Kano su yi la’akari da su yayin da suke tunanin makomar jihar.
Manufarmu ta Abba Kabir Yusuf Continuity Project ita ce hada kan masu kishin ci gaban Kano, domin ganin an ci gaba da tallafa wa manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jama’a.
Muna kira ga dukkan masu kishin Kano da su sanya Kano a gaba, su duba abin da ya fi amfani ga al’umma, sannan su goyi bayan ci gaba da shugabancin da suke ganin zai kai jihar ga wani sabon matsayi.
Kano tamu ce. Ci gabanta alhakinmu ne. Kishinta ya zama abin da ya hada mu.
Comrade Najeeb Nasir Ibrahim
Chairman, Abba Kabir Yusuf Continuity Project
