
Kungiyar Kano State APC Integrity Committee ta karrama Mai Girma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, da lambar yabo ta girmamawa, bisa irin kokarin da yake yi wajen haɗa kan ‘yan jam’iyyar APC, matasa da sauran al’ummar jihar.
Kungiyar ta bayar da wannan yabo ne a lokacin da tawagarta ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Ado Yello Mai TV, ta kai ziyarar girmamawa ga Kwamishina Waiya a ofishinsa.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, shugaban kungiyar ya yaba da irin rawar da Comrade Waiya ke takawa wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin ‘yan jam’iyyar, musamman matasa da sauran ƙungiyoyin siyasa da na al’umma.
Hon. Ado Yello Mai TV ya bayyana cewa kokarin Kwamishinan wajen kusantar jama’a da haɗa kan masu ruwa da tsaki na taimakawa matuƙa wajen ƙarfafa gwamnati da kuma samar da kyakkyawan yanayi domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da nata gudunmawa wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma mara wa gwamnati baya domin tabbatar da ci gaba da nasarorin da ake samu a Jihar Kano.
A nasa jawabin, Mai Girma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana godiyarsa ga shugabanni da mambobin kungiyar Kano State APC Integrity Committee bisa wannan ziyara ta girmamawa da suka kai masa.
Waiya ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki shi ne ginshiƙin nasarar kowace gwamnati da jam’iyyar siyasa.
Ya tabbatar wa kungiyar cewa zai ci gaba da aiki tare da su da sauran ƙungiyoyi masu kishin ci gaban Jihar Kano domin ƙarfafa manufofin gwamnati, inganta haɗin kai da kuma tabbatar da ci gaban jam’iyyar APC baki ɗaya.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga matasa da sauran ‘yan jam’iyyar da su rungumi zaman lafiya, haƙuri da fahimtar juna, yana mai cewa ci gaban Jihar Kano zai samu ne idan kowa ya bayar da tasa gudunmawa.
A ƙarshen ziyarar, kungiyar ta miƙa wa Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya lambar yabo ta girmamawa (Award of Excellence), inda ta bayyana shi a matsayin jagora mai jajircewa wajen haɗa kan jama’a da kuma bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Kungiyar ta ce karramawar wata hanya ce ta nuna godiya da yaba wa irin gudunmawar da Kwamishina Waiya ke bayarwa wajen ƙarfafa gwamnati, haɗa kan jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
