
Ƙungiyar Masu Sayar da Man Fetur Masu Zaman Kansu (IPMAN) ta yi gargaɗin cewa gidajen mai mambobinta za su daina sayar da fetur idan gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙarin tilasta musu sanya farashi na gwamnatin.
Sakataren Yaɗa Labaran ƙungiyar ba ƙasa, Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi ranar Talata.
Ya ce idan gwamnati ta tilasta wa masu sayar da mai bin farashin da ta gindaya, hakan na iya sa gidajen man su dakatar da sayar da fetur.

Waɗannan kalamai sun biyo bayan na Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, wanda ya yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta lamunci cin zarafin masu sayen fetur ta hanyar neman riba fiye da kima ko wasu hanyoyin da ke cutar da masu amfani da man fetur ba.
Lokpobiri ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin buɗe taron shekara ta 2026 na masu ba da shawara kan harkokin shari’a, wanda Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) ta shirya a Abuja.
Ministan ya ce ko da yake gwamnati ta daina kayyade farashin fetur kamar yadda ake yi a baya, hakan ba yana nufin hukumomin da ke kula da harkar za su yi watsi da alhakin kare haƙƙin masu amfani da man fetur ba.
Ya jaddada cewa tsarin kasuwa mai yanci ba ya hana gwamnati ɗaukar matakan da suka dace domin kare masu saye daga duk wani nau’i na cin zarafi.
