
Daga Munir Ibrahim Publisher
Kasancewar Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a cikin mutum uku da suka kai zagayen ƙarshe na rukunin Kwararrun Masu Sadarwa Kan Rikice-rikice (Crisis Communicator Category) a Kyaututtukan Kakakin Yada Labarai na Ƙasa na shekarar 2026, babban abin alfahari ne ba ga kwamishinan kaɗai ba har ma ga ɗaukacin Jihar Kano.
Wannan sanarwa na dauke ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Yuni, 2026, wadda Segun McMedal, Shugaban Kwamitin Shirya Kyaututtukan Kakakin Yada Labarai na Ƙasa, ya sanya wa hannu.
Kyautar, wadda Kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), masu wallafa PRNigeria da Spokespersons Digest ke shiryawa, ana kallonta a matsayin ɗaya daga cikin manyan dandamalin da ke duba ƙwarewa, gaskiya da tasiri a fannin sadarwa da hulɗar jama’a a Najeriya.
A cewar masu shirya gasar, gasar ta bana ta kasance ɗaya daga cikin mafi tsauri tun bayan ƙaddamar da kyautar. Daga cikin wadanda aka gabatar, guda 91 ne suka cika ƙa’idojin tantancewa, amma bayan kwakkwaran bincike da tantancewa, mutane da hukumomi 42 ne kawai suka samu shiga zagayen ƙarshe a rukunai 16 daban-daban.
Kwamitin alkalai ƙarƙashin jagorancin Farfesa Saudat Abdulbaqi ya gudanar da tantancewar ne bisa ma’auni irin su tasiri, kirkire-kirkire, sadarwa ga jama’a da kuma ingancin hujjojin da aka gabatar.

A rukunin masu sadarwa kan rikice-rikice, Waiya ya samu shiga cikin mutum uku na ƙarshe tare da Lere Olayinka na Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) da Dan Nwomeh na Gwamnatin Jihar Enugu.
Wannan gagarumar nasara tana nuna yadda ake ƙara yaba wa irin gudunmawar da Waiya ke bayarwa a fannoni kamar sadarwa, hulɗa da kafafen yaɗa labarai, mu’amala da masu ruwa da tsaki da kuma sarrafa bayanai a lokutan da ake fuskantar ƙalubale. Haka kuma, ta ɗora Kano a sahun jihohin da ake yabawa kan yadda suke tafiyar da harkokin yaɗa bayanai da sadarwa da jama’a.
Tun bayan hawansa wannan muƙami, Waiya ya yi ƙoƙari wajen inganta alaƙa tsakanin gwamnati da al’umma, ƙarfafa gaskiya da riƙon amana tare da bunƙasa hanyoyin isar da bayanan gwamnati ga jama’a.
Wannan karramawa ta ƙara shiga jerin lambobin yabo da girmamawa da kwamishinan ya samu daga ƙungiyoyi masu zaman kansu da na ƙwararru irin su NUJ, NIPR, NSB da ARCON.
Yayin da ake sa ran bayyana waɗanda za su lashe kyautar a watan Agustan 2026, Jihar Kano na da cikakken dalilin yin alfahari da wannan nasara. Ko da kuwa sakamakon ƙarshe ya kasance, samun Waiya a wannan matsayi wata babbar nasara ce ga Kano, gwamnatin jihar da kuma al’ummarta, wadda ke tabbatar da matsayin jihar a matsayin ɗaya daga cikin jagororin sadarwa da gudanar da bayanai a Najeriya.
