
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya buƙaci masana’antun siminti a faɗin ƙasar nan da su rage farashin siminti, yana mai cewa tsadar kayayyakin na kawo cikas ga ayyukan gine-ginen more rayuwa tare da haifar da ƙarin kuɗaɗen aiwatar da kwangiloli.
Umahi ya bayyana hakan ne a yayin taron ƙaddamar da sabon suna na kamfanin HBM, wanda a yanzu yake ƙarƙashin rukunin kamfanonin HUAXIN Group, da aka gudanar a birnin Lagos ranar Lahadi.
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara tattaunawa da masana’antun siminti daga ranar 1 ga watan Yuli domin nemo mafita kan matsalar tsadar siminti a ƙasar.

Haka kuma, ya buƙaci kamfanin HBM da sauran masana’antun siminti su ƙara ƙarfin samar da kayayyakinsu domin biyan buƙatun da ke ƙaruwa sakamakon manyan ayyukan raya more rayuwa da gwamnati ke aiwatarwa.
Umahi ya yaba wa kamfanin kan ci gaba da zuba jari a Najeriya tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba shi da sauran masu zuba jari goyon baya da haɗin gwiwa.
Ya kuma yi nuni da irin ci gaban da ake samu a fannin gine-gine da raya more rayuwa ƙarƙashin manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
