
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Bompai a Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu da Sunusi Ado Ma’aji, ta ɗage sauraron ƙarar da Malam Abduljabbar Kabara ya shigar kan Gwamnatin Jihar Kano zuwa ranar 29 ga watan Yunin 2026.

Rahotanni sun nuna cewa babban lauya Adamu Abubakar SAN tare da wasu lauyoyi huɗu ne ke kare Malam Abduljabbar Kabara, yayin da babban lauya Surajo Sa’ida SAN da Barrista Yakubu Abdullahi ke wakiltar Gwamnatin Jihar Kano.
A yayin zaman kotun, Malam Abduljabbar ya bayyana cewa tun a watan Janairun 2025 ya shigar da ɗaukaka ƙarar tare da gabatar da bayanansa a gaban kotu.
Sai dai lauyoyin gwamnatin jihar sun roƙi kotun da ta ba su ƙarin lokaci domin su kammala tare da shigar da nasu bayanan. Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta umarci lauyoyin gwamnati su gaggauta shigar da bayanansu tare da miƙa kwafi ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
Daga nan ne kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga Yunin 2026.
