
Daga Mohammed Babagana Abubakar
A kowace gwamnati mai nasara, akwai wani fagen gwagwarmaya da ba a gani da ido wanda sau da yawa shi ne ke ƙayyade nasara ko gazawar shugabanci. Wannan gwagwarmaya ba ta faruwa a majalisa ko dandamalin yaƙin neman zaɓe, sai dai a cikin da’irar mutanen da ke zagaye da shugaba. Ingancin mutanen da ke samun damar kai wa gwamna shawara na da tasiri matuƙa wajen tsara manufofi, gudanar da gwamnati, da kuma irin tarihin da za a tuna da gwamnatin.
Yayin da siyasa ke ƙara ɗaukar salo iri iri kuma sha’awar samun kusanci da mulki ke ƙaruwa, ya zama wajibi a bambance tsakanin rukuni biyu da ke fafatawa wajen samun tasiri a wajen shugabanni. Akwai masu kishin gwamnati na gaskiya waɗanda ke son ganin gwamnati ta yi nasara, sannan akwai masu cin moriyar mulki yan chori waɗanda ke kallon gwamnati a matsayin wata hanya ta biyan buƙatun kansu da samun ribar siyasa.
Tarihi ya nuna sau da dama cewa babbar barazanar da ke fuskantar kowace gwamnati mai aiki ba lallai ba ce ta fito daga hamayya, sai dai daga mutanen da ke cikin tsarin mulki waɗanda ke fifita muradunsu na kashin kai a kan muradun jama’a. Irin waɗannan mutane kan fito da sunan masu biyayya ga shugabanci, amma a zahiri suna raunana manufofin da suke iƙirarin karewa.

Daya daga cikin manyan matsalolin da irin wannan yanayi ke haifarwa shi ne cutar da cigaban shugabani . Masu irin wannan dabi’a ba sa zuwa da tsare tsaren ci gaba ko hanyoyin magance matsalolin al’umma. Abin da suka fi ƙwarewa a kai shi ne yawan yabo mara amfani, ɓoye gaskiya, da ƙirƙirar rikice rikicen siyasa domin cimma muradunsu.
Burinsu ba wai ƙarfafa shugabanci ba ne, sai dai mallake damar isa ga shugaba domin su ci gaba da amfana. Sau da yawa suna hana gaskiya isa ga shugaba, suna kawar da duk wani ra’ayi da zai iya gyara kura kurai, tare da gina wani yanayi da ake son shugaba ya ji abin da yake so kawai.
Idan aka bar irin wannan yanayi ya daɗe, yana iya haifar da matsaloli masu yawa. Yanke hukunci zai fara dogaro ne da bayanan da ba su cika ba, yayin da muradun jama’a za su fara zama na biyu bayan bukatun masu neman gata da kusanci da mulki.
Sakamakon hakan kuwa ba ya ɓoyewa. Lokacin da gwamnati ta fara sauraron masu yi mata kirari fiye da ƙwararrun masu ba da shawara, abubuwan da suka kamata su zama fifiko kamar gina tituna, bunƙasa ilimi, ƙarfafa harkokin lafiya, noma, da samar wa matasa ayyukan yi kan fara fuskantar koma baya. Maimakon mayar da hankali kan ci gaban jama’a, gwamnati za ta tsinci kanta cikin kula da rikice rikicen da aka ƙirƙira da kuma rabon gata ga wasu tsirarun mutane.
Ga duk wani gwamna mai hangen nesa wanda ke son sauya rayuwar jama’a ta hanyar ayyukan ci gaba, wannan babbar barazana ce. Domin shugabanci na gaskiya yana buƙatar mayar da hankali, tsari, da hangen nesa. Ba zai yiwu a samu irin wannan ci gaba ba idan masu son amfana da mulki ne ke tsara ajanda.
A gefe guda kuma akwai masu kishin gwamnati na gaskiya. Waɗannan su ne mutanen da biyayyarsu ba ta ta’allaka kan abin da za su samu ba, sai dai kan nasarar manufofin gwamnati da walwalar al’umma. Sun fahimci cewa biyayya ta gaskiya ba tana nufin amincewa da komai ba ne, sai dai taimakawa shugaba wajen yanke mafi kyawun hukunci.
Masu irin wannan hali suna da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa gwamnati.
Na farko, suna da hangen nesa. Sun san cewa tarihin gwamnati ba ya ta’allaka kan nasarorin siyasa na yau da kullum, sai dai kan ayyukan ci gaba da za su amfani al’umma na dogon lokaci.
Na biyu, suna ba da shawara ta gaskiya kuma mai tushe. Ba sa tsoron faɗin gaskiya idan akwai kuskure. Sun fahimci cewa gyara kuskure tun kafin ya zama matsala ya fi anfani fiye da yabo marar amfani.
Na uku, suna da alaƙa da talakawa. Suna sauraron matsalolin jama’a tare da tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun dace da buƙatun al’umma, ba wai son zuciyar wasu tsirarun mutane ba. Ta haka ne suke zama gada tsakanin gwamnati da jama’a.
Saboda haka, babban ƙalubalen kowace gwamnati shi ne gano bambanci tsakanin waɗanda suke son bayar da gudummawa da waɗanda suke son cin moriyar kawai. Wannan na buƙatar a tace hanyoyin samun tasiri a wajen shugabanci, tare da tabbatar da cewa cancanta, ƙwarewa, gaskiya da kishin ci gaba ne kawai suke zama mabuɗin samun kusanci da gwamnati.
Babban ƙarfin gwamna ba ya cikin yawan mutanen da ke yi masa kirari, sai dai cikin yawan mutanen da ke shirye dasu taimaka masa da shawara mai amfani domin ya yi nasara. Shugabanci yana bunƙasa ne idan mutanen kirki, masu hangen nesa da kishin ci gaba ne ke kewaye da shi, ba masu neman anfani na kashin kai ba.
A ƙarshe, ba kalaman siyasa ko surutan kafafen sada zumunta ba ne za su tantance nasarar kowace gwamnati. Abubuwan da za su yi magana su ne titunan da aka gina, makarantun da aka inganta, asibitocin da aka ƙarfafa, ayyukan yi da aka samar, da rayukan jama’ar da aka canza.
Don haka, duk wani shugaba da ke son barin tarihi mai kyau dole ne ya kauce wa surutan masu cin moriyar mulki, ya guji cutar yabo da riƙon makafi, sannan ya bada dama ga masu kishin gwamnati na gaskiya waɗanda biyayyarsu ta ginu kan ƙwarewa, gaskiya da sadaukarwa ga ci gaban al’umma. Ta haka ne kawai gwamnati za ta ci gaba da tafiya a kan turbar da ta dace wajen kawo cigaba da samar da sahihan ribar dimokuraɗiyya ga jama’a.
