
Sirrin Shahararsa da Kuma Fitaccen Salon Jagorancin Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin Kabo CFR, PhD, FCNA
✍️ Rubutun Sufyan Lawal Kabo (Sefjamil)
Mutane da dama suna ta tambaya: me ya sa mai girma Sanata Barau I. Jibrin Kabo yake ci gaba da zama daban a cikin ƴan siyasar Najeriya? Me ya sa al’ummar Kano ta Arewa suke ci gaba da goya masa baya, suke tsayawa tsayin daka suce sai shi, a koda yaushe, duk da ƙalubalen siyasa da na ƴan adawa?
Tun daga lokacin da ya wakilci Tarauni a Majalisar Wakilai, zuwa lokacin da ya zama Kwamishinan Sadarwa na Jihar Kano, daga bisani Sanatan Kano ta Arewa tun shekarar 2015, har zuwa matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da yake kai a yau, abu guda ya bayyana ƙarara: Barau ya fita daban a cikin ƴan siyasa, saboda shi ɗin na daban ne.
Ku biyo ni domin in bayyana muku sirrin da ya sa “Maliya” ya zama na musamman.
1. Gaskiya, Tsoron Allah, Riƙon Amana Da Son Jama’a:
Babban sirrin nasarar Sanata Barau shi ne gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah.
Barau ya yi imani cewa shugabanci amanar Allah ne, kuma duk shugaba sai ya tsaya gaban Ubangiji ya yi bayani kan yadda ya jagoranci al’umma. Salon jagorancin Sanata Barau I. Jibrin Kabo yana kamanceceniya da jagoranci irin na Sayyidina Umar bn Khattabi, yana jin tsoron gamuwa da Allah ace ya gaza yiwa al’ummar da yake jagoranta adalci.
Na kusa da Barau sun sha bada labarin cewa a lokuta da dama yakan miƙa wasu damarmaki ga bare su soma cin gajiyar abu, ya haƙurƙurtar da na kusa dashi har zuwa wani lokaci da wasu damarmakin zasu kuma bijirowa. Yafi samun natsuwa idan ya amfanar da al’umma suka samu ci gaba. Barau yana yawan ƙarfafawa waɗanda yake tare dasu guiwa wajen kwatanta irin wannan kyakkyawar dabi’a tasa.
2. Ƙwarewa, Ilimi da Kuma Gogewa:
Shugabanci ba surutu ba ne, yana buƙatar ilimi, ƙwarewa, kuma Barau ya haɗa su gaba ɗaya. Sanata Barau I. Jibrin Kabo mutum ne mai zurfin ilimi a fannin Lissafi, ilimin gudanar da kuɗi (Financial Management), ilimi a harkar kasuwanci (Business Administration) da sana’o’i na zamani (Corporate Entrepreneurship) har zuwa matakin Digirin Digirgir da phD sannan uwa uba, mutum ne mai ilimin addini.
Tun ma kafin ya shiga harkar siyasa ka’in da na na’in ya yi aiki a bangarori masu zaman kansu da kuma na gwamnati inda ya samu gogewa sosai.
A fannin siyasa, Barau yana ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da suka daɗe suna tasiri tun daga 1999. A Majalisar Tarayya ya yi aiki a muhimman kwamitoci da suka haɗa da kwamitin kasafin kuɗi, harkokin mai, ilimi mai zurfi da harkokin ‘yan sanda.
A yau, matsayin da yake kai na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya ba shi damar gina alaƙa mai ƙarfi a cikin gida da wajen Najeriya.
Mutum mai irin wannan gogewa bazai yiwu ace ya gaza ba.
3. Kishin Ƙasa da Jarumtaka:
Barau mutum ne mai tsananin kishin Arewa da Najeriya baki ɗaya, ya ɗauki wannan ƙasa tamu da matuƙar muhimmanci, ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya sannan a koda yaushe shirye yake ya kare mutuncin ƙasar nan a idon duniya.
‘Yan Najeriya sun shaida haka a wani lokaci a baya cikin zauren Majalisar Dattawa lokacin da ake tattaunawa kan kalaman matsin lambar Shugaban Amurka Donald Trump a kan Najeriya.
A yayin muhawarar, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya nuna tsoron da takatsantsan wajen mayar da martani kai tsaye ga Trump saboda yanayin diflomasiyya, har aka jiwoshi yana cewa: “Ni a su wa da zan mayar wa Trump martani?” Sai dai Barau cikin ƙarfin hali ya katse maganar tare da bayyana cewa shi ba ya jin tsoron faɗar gaskiya zai kare mutuncin Najeriya.
Ya bayyana ƙarara cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ƴanci, kuma bai kamata ƴan Najeriya su ji tsoron bayyana matsayinsu ga kowace ƙasa ba. Har ma ya ce: “Ba na shakkar Trump. Najeriyar mu ƙasa ce mai cikakken ‘yanci.”
Wannan furuci ya ba mutane mamaki domin ba kasafai ake ganin manyan shugabanni suna nuna irin wannan ƙwarin gwiwa wajen kare mutuncin ƙasa ba.
Ga mutane da dama, wannan ba siyasa kawai ba ce, alama ce ta jarumtaka, kishi da kuma kare martabar Najeriya. Wannan ne ya sa mutane da dama suke ƙara ganin girman Sanata Barau I Jibrin Kabo, suke martaba shi.
4. Ya Shigo da Tsari da Manufa:
Wasu shugabanni kan shigo tsarin mulki ba tare da sun shirya masa ba, amma shi ya shigo da cikakken tsari da manufofin sa.
Tun kafin ya zama Sanata, babu abinda ke damun Barau kamar yadda ya sha faɗe a wancan lokaci, irin halin tsananin talauci, rashin ilimi da rashin ababen more rayuwa da suka addabi al’umma musamman al’ummar yankin da ya fito na Kano ta Arewa.
Wannan ne yasa yana hayewa kujerar wakilci, ya soma aiwatar da aiyukan alkhairi ga jama’ar sa, yayi ta kawar da matsalolin al’umma ɗaya bayan ɗaya cikin nasara. Barau bai shiga ofis domin neman sa’a ba kamar yadda akasarin shuwagabanni suke yi, ya shiga ne da kyawawan manufofi.
5. Inganci da Nagartar Aiyukan Sa:
Wani babban dalilin da ya sa ya bambanta shi ne irin ingancin da nagartar ayyukansa. Barau bai yarda da jigari jigarin aiki ba, ba yana aiyuka bane kawai dan ace yana aiki, a’a, yana aiyuka ne na Mahadi Ka Ture, irin aiyukan da al’ummar zasu dauki shekaru aro aro suna amfana.
Wannan dalili ne yasa ayyukansa a bangarorin shimfiɗa tituna, ilimi, lafiya, sufuri, wasanni da tallafawa jama’a da sauran su suka fita dabam a Kano ta Arewa da ma wajenta. Dubban matasa da mata sun amfana da tallafin karatu, kyautar motoci, babura, tallafin jari don yin kasuwanci da sauran su. Alumai na dukkanin Garuruwa da unguwanni dake yankin Kano ta Arewa sun daɗe dumu dumu cikin Alkhairi a dalilin nagartaccen wakilcin Barau I. Jibrin Kabo.
Ta dalilin Barau FC da ragowar ci gaba da ya kawo, matasa da dama sun samu dama da mafita a rayuwa.
6. Jinƙai da Ayyukan Alheri Ba Tare da Nuna Bambanci Ba:
Duk da Kano ta Arewa yake wakilta, ayyukan jin ƙai irin na Barau, ba a iya yankin sa na Kano ta Arewa suka tsaya ba, a kodayaushe Barau yana fafutukar kare mutunci da tsayawa don karɓo hakkin al’ummar jihar Kano, yankin Arewa da ma na Najeriya gabaki ɗaya. Wannan hoɓɓasa irin nasa ne ya janyo farin jininsa ke ƙara haɓɓaka da yaɗuwa tsakankanin ƴan Najeriya, ake yawan zancen sa ake kuma yabawa tasiri da salon wakilcinsa.
7. Siffofinsa na Jagoranci:
Barau yana da muhimman siffofin shugabanci. Mutum ne mai nutsuwa, hikima na wakilci, mutum ne mai haƙuri, yana da jajircewa da tsayawa tsayin daka akan domin tabbatar da aiyukan alkhairin da ya sanya a gaba. Abin da ya bambanta shi da wasu ‘yan siyasa shi ne daidaito da balagar siyasa.
Waɗannan halaye ne suka taimaka masa yayi ta samun ci gaba, yayi ta ɗarewa matakai daban daban duk da ƙalubalen da yayi ta fuskanta da ƴan adawa irin na siyasa.
8. Tawali’u da Sauƙin Kai
Abin da wataƙila zai fi baiwa mutane al’ajabi game da Barau shi ne tawali’u da sauƙin kansa tun daga sadda ya soma hawa matakai daban daban na ɗaukaka har i zuwa matsayin da yake kai a yau na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Barau kanyi mu’amala da na ƙasa dashi da dukkanin al’umma sa da talakawa na koina cikin sauƙin kai da girmamawa. Kowa nashi ne, baya wulaƙanta ɗan Adam. Ko kaɗan bai yarda ɗaukakar da ya samu a rayuwa ta canja halayensa na kirki, na ƙauna da tausayin al’umma ba. Wannan tawali’u ne yasa mutane a kullum ke shauƙin Sanata Barau I.Jibrin Kabo suke alfahari dashi.
Waɗannan dalilai da na zayyana a sama, kaɗan ne daga cikin halayen Sanata Barau I. Jibrin Kabo da suka janyo masa farin jini a tsakarkanin al’ummar da ta Kano ta Arewa, Jihar Kano, Arewacin Najeriya da ma Najeriyar gabaki ɗaya.
Wannan shi yasa fatan al’umma a kodayaushe shine, su kuma zaɓen Sanata Barau ya koma kujerar Sanatan Kano ta Arewa karo na huɗu a shekarar 2027, a majalisar dattawa ya sami kujerar Shugaban Majalisar Dattawa (Senate President), yazo yayi Gwamnan Jhar Kano na shekara takwas, sannan ya haye kujerar Shugaban Ƙasar Najeriya a 2039 inshaAllahu.
Wannan, a taƙaice su suka sanya DSP Barau I. Jibrin Kabo ya zama na daban.
Sufyan Lawal Kabo Senior Legislative Aide (SLA) ne ga DSP Barau I. Jibrin Kabo, kuma shine Daraktan BARAU timeLINE GROUP (BtG)
