
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Miga, Honarabul Sa’idu Yusuf Miga, wanda ya shafe tsawon shekaru 16 yana wakiltar al’umma a Majalisar Tarayya, ya rasa damar komawa majalisar jihar karo na farko tun bayan zaɓensa.
Rahotanni sun nuna cewa Hon. Miga ya kasa samun tikitin sake tsayawa takara domin komawa kujerarsa, lamarin da ya zo da mamaki ga magoya bayansa da masu bibiyar harkokin siyasa a jihar.
Sa’idu Yusuf Miga na daga cikin fitattun ‘yan siyasar Jigawa da suka yi dogon lokaci a Majalisar Dokokin Tarayya, inda ya taka rawa wajen gabatar da kudurori da ayyukan ci gaba ga al’ummarsa.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa rashin samun tikitin nasa na nuni da yadda siyasar cikin gida ke ci gaba da sauyawa, tare da bai wa sabbin ‘yan takara damar fitowa a dama da su.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Hon. Miga bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da rashin samun tikitin ko matakin da zai dauka a gaba.
