Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Business
  • Education
  • Featured
  • Health
  • Politics
  • Sports
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook Instagram TikTok
BROWN PIGEON MEDIA
SUBSCRIBE
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    FEDERAL GOVERNMENT SUSPENDS PROPOSED WAEC, NECO REGISTRATION FEE HIKE

    July 13, 2026

    FG: FANNIN MA’ADANAI YA JAWO JARIN DALA BILIYAN 3 CIKIN SHEKARU UKU

    June 18, 2026

    GWAMNATIN TARRAYYA TA MUSANTA SHIRIN SOKE HUKUMAR NBAIS

    June 18, 2026

    DEMOCRACY DAY SPEECH: OUR GENERATION MUST SECURE PROSPERITY 

    June 12, 2026

    Senator Barau Reaffirms ECOWAS Parliament’s Commitment to Regional Unity at Commissioning of New ECOWAS Headquarters

    July 3, 2026

    DA DUMI-DUMI: Starmer ya yi Murabus Daga Mukamin Firaministan Birtaniya

    June 22, 2026

    NETANYAHU YA SHA ALWASHIN HANA IRAN MALLAKAR MAKAMIN NUKILIYA

    June 13, 2026

    Girgizar Ƙasa Mai Ƙarfi Ta Hallaka Mutane a Philippines, Ana Fargabar Tsunami a Wasu Ƙasashe

    June 8, 2026

    ABBA KABIR YUSUF: A GENTLEMAN OF INTEGRITY AND THE IMPORTANCE OF HEARING BOTH SIDES

    November 24, 2026

    WAIYA UNVEILS PLAN TO EMPOWER OVER ONE MILLION YOUTHS, SEEKS STRONGER PARTNERSHIP WITH NORTHERN YOUTH ASSEMBLY

    November 24, 2026

    WAIYA ASSURES KANO STATE YOUTH PARLIAMENT OF INAUGURATION THIS MONTH

    November 23, 2026

    WAIYA INAUGURATES NEW POLITICAL NETWORK, PROMISES SUPPORT FOR GRASSROOTS DEVELOPMENT

    November 23, 2026
  • Business

    KANO EXPLORES REGIONAL TRADE PARTNERSHIPS, INVESTMENT OPPORTUNITIES

    November 16, 2026

    KASEDA TA GUDANAR DA SHIRIN WAYAR DA KAI GA MSMEs KAN KA’IDOJIN NAFDAC A JIHAR KATSINA

    June 12, 2026

    Dangote Industrialising Africa– NCCIMA DG

    May 17, 2026

    INEC TA BUKACI MASU RIJISTAR KATIN ZABE A KANO DA SU JE SU DUBA SUNAYENSU

    April 27, 2026

    KANO TO HOST NATIONAL LAUNCH OF ECoN INITIATIVE, SET TO DRIVE INNOVATION AND INDUSTRIAL GROWTH IN NORTH-WEST

    April 16, 2026
  • Education

    WAIYA URGES STUDENTS TO UPHOLD DISCIPLINE, PATRIOTISM AT INDEPENDENCE ANNIVERSARY

    October 2, 2026

    WAIYA COMPLETES PhD VIVA VOCE, EARNS NEW ACADEMIC DISTINCTION

    September 22, 2026

    Gov. Yusuf Reaffirms Education Priority, Commends Al-Istiqama University’s Impact

    September 19, 2026

    KANO RANKS FIRST IN EDUCATION SPENDING, SECOND IN CLIMATE GOVERNANCE

    September 13, 2026

    KANO GOVERNMENT INAUGURATES 14-MEMBER COMMITTEE TO OVERSEE HANDOVER OF SORTED RANO FACILITIES TO FEDERAL POLYTECHNIC

    September 11, 2026
  • Featured

    Kano State Government Organises Two-Day Retreat for Online Media Publishers in Jigawa

    January 15, 2026

    Former Kano APC Councilors Hold Special Prayers for Governor Abba Kabir Yusuf

    October 27, 2025

    Mustapha Salisu Makes Azerbaijan Move

    September 9, 2025

    Delta 2025 NYG: Team Kano Finish 9th With 14 Medals

    September 8, 2025

    Kano Government Clarifies Position on Elders Council, Backs Its Own Initiative

    September 7, 2025
  • Health

    KANO GOVERNMENT APPROVES IMMEDIATE PAYMENT OF MRTF ALLOWANCE TO 90 DOCTORS, BEGINS PROCESS FOR FEDERAL SALARY ALIGNMENT

    October 30, 2026

    HEALTH SECTOR REFORMS: HOW KANO STATE IS TRANSFORMING HEALTHCARE DELIVERY

    October 29, 2026

    NORTH-WEST DEVELOPMENT COMMISSION TEAMS UP WITH DALA ORTHOPAEDIC HOSPITAL TO EASE MEDICAL COSTS

    August 1, 2026

    Kano Government Targets Maternal Mortality with 484 New Mini-Ambulances for Rural Wards

    June 19, 2026

    Gwamnatin Kano Ta Sayi Ƙananan Motocin Asibiti 484 Domin Taimaka wa Mata Masu Juna Biyu – Kwamishinan Lafiya

    June 19, 2026
  • Politics

    2027: YOUTH COMMISSIONER INAUGURATES WAIYA POLITICAL NETWORK, VOWS SUPPORT FOR APC

    November 24, 2026

    IGBO COMMUNITY IN KANO REAFFIRMS SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA KABIR YUSUF AHEAD OF 2027 GENERAL ELECTION

    November 23, 2026

    NYA HAILS WAIYA’S NOMINATION AS AREWA FOR ASIWAJU DEPUTY DIRECTOR

    November 20, 2026

    WAIYA RECEIVES APPOINTMENT LETTER AS DEPUTY DIRECTOR III, ENGAGEMENT WITH CIVIL SOCIETY AND SUPPORT GROUPS, AREWA FOR ASIWAJU

    November 20, 2026

    PRESIDENT TINUBU WARNS AGAINST POLITICAL VIOLENCE, CALLS FOR ISSUE-BASED CAMPAIGNS AHEAD OF 2027 ELECTIONS

    November 13, 2026
  • Sports

    Waiya Visits Trumpet Football Academy, Urges Young Players to Embrace Professionalism

    November 16, 2026

    WAIYA, SPORTS COMMISSION BOARD MEET OVER KANO SPORTS DEVELOPMENT*

    November 14, 2026

    KANO STATE GOVERNMENT SPONSORS KANO RENEWED HOPE CUP FOR U-19, U-17 AND U-15 TEAMS

    November 12, 2026

    Holy Cross Wins 2026 Bishop Olympic Games as Kano Sports Commissioner Waiya Joins Grand Finale

    November 9, 2026

    𝐊𝐰𝐚𝐦𝐢𝐬𝐡𝐢𝐧𝐚 𝐖𝐚𝐢𝐲𝐚 𝐘𝐚 𝐊𝐚𝐢 𝐙𝐢𝐲𝐚𝐫𝐚 𝐆𝐚 𝐌𝐚𝐢 𝐓𝐬𝐚𝐫𝐨𝐧 𝐑𝐚𝐠𝐚𝐫 𝐊𝐚𝐧𝐨 𝐏𝐢𝐥𝐥𝐚𝐫𝐬 𝐔-𝟏𝟗 𝐃𝐚 𝐘𝐚 𝐉𝐢 𝐑𝐚𝐮𝐧𝐢, 𝐘𝐚 𝐘𝐢 𝐀𝐥𝐤𝐚𝐰𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐁𝐢𝐲𝐚𝐧 𝐊𝐮ɗ𝐢𝐧 𝐘𝐢 𝐌𝐚𝐬𝐚 𝐓𝐢𝐲𝐚𝐭𝐚 𝐆𝐚𝐛𝐚 Ɗ𝐚𝐲𝐚

    November 8, 2026
  • Videos
  • More
    • About Us
    • Contact Us
    • Privacy Policy
BROWN PIGEON MEDIA
Home » DAGA NAƊAƊƊE ZUWA MAI TAYAR DA HANKALI: BINCIKEN GASKIYAR MANUFOFIN DA KE BAYAN HARE-HAREN GALADIMA GA GWAMNA YUSUF DA DSS
Politics

DAGA NAƊAƊƊE ZUWA MAI TAYAR DA HANKALI: BINCIKEN GASKIYAR MANUFOFIN DA KE BAYAN HARE-HAREN GALADIMA GA GWAMNA YUSUF DA DSS

Brown Pigeon MediaBy Brown Pigeon MediaMarch 2, 20265 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp Telegram Email Copy Link

 

Daga Mohammed Babagana Abubakar

 

 

A dandalin siyasar Nijeriya, akwai wasu ‘yanwasa da suka kware wajen abin da masu nazari ke kira dabarar kawar da hankali: wato haifar da hayaniya mai yawa kan zargin rashin adalci a daidai lokacin da tasirinsu a siyasa ke dusashewa. Kalaman da Alhaji Buba Galadima ya rika yi a baya-bayannan kan Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, da kuma Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS a Kano, misali ne karara na wannan salo. Zarge-zargen rashin adalci da kuma kama masu adawa da gwamnati da cewar ana farautarsu na nuna tamkar jihar na cikin rikici. Amma idan aka yi duba na gaskiya da idon basira, labarin ya sha bamban matuƙa.

 

Ba abin mamaki ba ne cewa hare-haren Galadima sun ƙaru nan take bayan cire shi daga kujerar Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano State Polytechnic) a watan Fabrairu 2026. Gwamna Yusuf, bisa manufarsa ta Kano First Agenda, wani tsarin gudanar da mulki da ke mayar da hankali kan inganta cibiyoyi da fifita ci gaban Kano, ya sauke Galadima daga mukamin, yana mai nuni da bukatar inganta aiki da sake farfaɗo da cibiyar. Daga bisani, aka naɗa Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir, wanda darajarsa da kusancinsa da al’umma suka dace da burin sake fasalin da Gwamnan ke nema.

 

Ga mutumin da ya riƙe babban mukami a wata jiha da ba jiharsa ba, abin da ya fi dacewa shi ne barin mukamin cikin mutunci da kima. Amma maimakon haka, Galadima ya zaɓi ramuwar gayya. Kamfen dinsa na kafafen yaɗa labarai, wanda ke ƙaruwa a kowace hira, ba dabi’ar mai fafutukar dimokuraɗiyya ba ce. Dabi’a ce ta wanda aka cire masa damar cin moriyar mukami, kuma yake son ya sa a biya farashin siyasa kan hakan.

 

Zarge-zargen da Galadima ya yi, ciki har da batun kama wani mai shirin rediyo da kuma bayyana matakan jami’an tsaro a matsayin tsangwama ta siyasa, ƙoƙari ne na karkatar da gaskiyar tsarin mulki da aikace-aikacen gwamnati a Kano. A halin yanzu, Kano na tafiya a cikin yanayi mai sarkakiya ta fuskar tsaro da siyasa, musamman ma bayan da Gwamnan ya yi sauyin sheka ta siyasa zuwa APC, wanda ya buƙaci daidaita siyasar jihar cikin sabon yanayin ikon ƙasa. A irin wannan yanayi, ayyukan DSS suna gudana ne bisa dokar tarayya, hurumin hukuma, da kuma sahihan korafe-korafe, ba bisa umarnin siyasa ba.

 

‘Yancin faɗin albarkacin baki, wanda Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada, hakki ne da gwamnatin Gwamna Yusuf ta mutunta. Amma babu wani sashe na kundin da ke bai wa mutum damar amfani da kafafen yaɗa labarai don tunzura rikici, yada ƙarya da aka tabbatar, ko aikata laifukan da Dokar Yaki da Laifukan Yanar Gizo (Cybercrime Act 2015) ta haramta. Idan jami’an tsaro suka gayyaci wani domin amsa tambayoyi bisa sahihancin korafe-korafe a ƙarƙashin wannan doka, wannan aiki ne na bin doka da oda. Kiransa da “garkuwa ta siyasa” ba fafutukar dimokuraɗiyya ba ce; misali ne na ɓata suna da gangan.

 

Yayin da Galadima ke gina labarin tsangwama, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina abin da ya fi muhimmanci, rikodin mulki. Gwamnatin ta fara gyaran manyan makarantun gaba da sakandare na jihar, tana magance matsalolin da suka daɗe suna faruwa. Ta ɗauki matakan biyan basussukan garatuti ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, alƙawarin da gwamnatocin baya suka kasa cikawa. Haka kuma, ta fara rushe tsarin siyasar ubangida, inda aka daɗe ana mayar da cibiyoyin gwamnati tamkar mallakin masu iko maimakon al’umma.

 

Wannan rushewar tsarin siyasar gata ne da ke bayyana ainihin dalilin da ke bayan kamfen ɗin Galadima. Ba wai ya ƙi tsarin mulkin Gwamna Yusuf ba ne; abin da yake ƙi shi ne sabon yanayin da ba ya ba da tabbacin samun mukamai da tasiri bisa alaƙar siyasa kaɗai. Cire shi daga kwalejin ba kawai sauyin aiki ba ne; alama ce cewa tsoffin tsare-tsare sun ƙare. Martaninsa kuwa shi ne ƙoƙarin nuna cewa irin waɗannan matakai suna da tsada a siyasa. Amma Gwamna Yusuf da gwamnatinsa dole ne su ci gaba da tafiya ba tare da gezau ba.

 

Al’ummar Kano ba kawai kallo suke ba, kuma ba za a yaudare su ba. Suna da wayewar siyasa da tarihin fahimta mai zurfi, kuma suna iya bambance tsakanin fafutukar dimokuraɗiyya ta gaskiya da siyasar ƙorafi wadanda suka rasa madogara. Galadima ba ya yaƙi ne don talakawan Kano; yana yaƙi ne don mukami da aka raba shi da shi, gata da aka janye, da tasirin siyasa da ya rasa. Wannan haƙƙinsa ne. Amma ya kamata a kira shi da sunansa na gaskiya.

 

An zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf ne domin ya yi mulki bisa muradun al’ummar Kano, ba don kiyaye damar gata ta wasu ba. Gwamnatinsa, DSS, da dukkan cibiyoyin da ke aiki bisa hurumin kundin mulki dole ne su ci gaba da mai da hankali kan wannan manufa, ba tare da shagaltuwa da hayaniyar masu jin zafin rasa gata ba. Makomar Kano za ta ginu ne da nagartaccen mulki, aiki tukuru, da rikon amana, ba kan ƙorafe-ƙorafen da aka ƙirƙira domin dawo da tsohuwar daula ba.

 

 

GAME DA MARUBUCIN

Mohammed Babagana Abubakar mai sharhi ne kan siyasa da nazarin al’amuran mulki, mai sha’awar batutuwan rikon amana, ingantaccen shugabanci, da ci gaban dimokuraɗiyya a Kano da Arewacin Nijeriya.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email VKontakte WhatsApp Copy Link
Previous ArticleIran Ta Tabbatar Da Kisan Ali Khamenei Da Iyalansa By Mutawakkilu
Next Article Ba boyayyen abu ba ne cewa siyasar Kano ba ta taɓa zama al’ada ba

Related Posts

2027: YOUTH COMMISSIONER INAUGURATES WAIYA POLITICAL NETWORK, VOWS SUPPORT FOR APC

November 24, 2026

IGBO COMMUNITY IN KANO REAFFIRMS SUPPORT FOR GOVERNOR ABBA KABIR YUSUF AHEAD OF 2027 GENERAL ELECTION

November 23, 2026

NYA HAILS WAIYA’S NOMINATION AS AREWA FOR ASIWAJU DEPUTY DIRECTOR

November 20, 2026

WAIYA RECEIVES APPOINTMENT LETTER AS DEPUTY DIRECTOR III, ENGAGEMENT WITH CIVIL SOCIETY AND SUPPORT GROUPS, AREWA FOR ASIWAJU

November 20, 2026

PRESIDENT TINUBU WARNS AGAINST POLITICAL VIOLENCE, CALLS FOR ISSUE-BASED CAMPAIGNS AHEAD OF 2027 ELECTIONS

November 13, 2026

False, Reckless and Shameful Allegations by the Newly Appointed Kano State Commissioner for Information.

November 10, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Stay In Touch
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • Telegram
  • WhatsApp
Latest Posts

2027: YOUTH COMMISSIONER INAUGURATES WAIYA POLITICAL NETWORK, VOWS SUPPORT FOR APC

By Brown Pigeon MediaNovember 24, 2026

By Abdu Saidu The Kano State Commissioner for Youth and Sports Development, Comrade…

ABBA KABIR YUSUF: A GENTLEMAN OF INTEGRITY AND THE IMPORTANCE OF HEARING BOTH SIDES

November 24, 2026

WAIYA UNVEILS PLAN TO EMPOWER OVER ONE MILLION YOUTHS, SEEKS STRONGER PARTNERSHIP WITH NORTHERN YOUTH ASSEMBLY

November 24, 2026

WAIYA ASSURES KANO STATE YOUTH PARLIAMENT OF INAUGURATION THIS MONTH

November 23, 2026

WAIYA INAUGURATES NEW POLITICAL NETWORK, PROMISES SUPPORT FOR GRASSROOTS DEVELOPMENT

November 23, 2026
© 2026 Brown Pigeon Media. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.