
Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano ya fitar da sanarwar zagaye (Circular No. 4/2026) mai ɗauke da ranar 25 ga Yuni, 2026, inda ya sanar da ƙaddamar da shiri na musamman na rajistar katin zaɓe ga ma’aikatan gwamnati da iyalansu masu shekaru 18 zuwa sama.
A cewar sanarwar, an tanadi cibiyar rajista ta musamman a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da ke Audu Bako Secretariat, Kano, domin sauƙaƙa wa ma’aikatan gwamnati da iyalansu damar yin rajistar katin zaɓe cikin sauƙi.

Za a gudanar da rajistar daga Litinin, 29 ga Yuni zuwa Juma’a, 3 ga Yuli, 2026, tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a kowace rana.
Sanarwar ta jaddada cewa rajistar katin zaɓe hakki ne na kowane ɗan ƙasa da ya cancanta, tare da ƙarfafa ma’aikatan gwamnati da iyalansu su yi amfani da wannan dama. Haka kuma, ta bayyana cewa rajistar zataci gaba da kasancewa har zuwa ranar 10 ga Yuli, 2026
