
Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi, ta jawo ce-ce-ku-ce bayan wata kalama da ta yi dangane da zargin da ake yi wa mutane kan zama a otal-otal.
A wata sanarwa da ta wallafa, Nafisat ta ce idan har zama a Hotel ana kallonsa a matsayin iskanci, to ya kamata a ce duk masu zuwa aikin Hajji ma ‘yan iska ne, domin galibin mahajjata suna sauka ne a otal-otal da ke kewaye da Masallacin Harami.

Jarumar ta bayyana cewa akwai otal-otal da dama da suka mamaye yankunan da ke kusa da Ka’abah, inda maza da mata ke sauka a cikinsu domin gudanar da ibadunsu, ba tare da wani ya ɗauki hakan a matsayin iskanci ba.
Tace, “Hotel-Hotel ne suka kewaye ɗakin Ka’abah gaba ɗaya, kuma mata da maza ne suke zama a ciki. Shin me ya sa idan ka je can ba a kallon iskanci za ka yi ba, amma idan ka je sauran Hotel sai a ɗauka haka ne?”
Kalaman nata sun haifar da martani mabambanta a kafafen sada zumunta, inda wasu suka goyi bayan hujjar da ta gabatar, yayin da wasu kuma suka soki yadda ta kwatanta batun da aikin Hajji.
Rahotanni na nuna cewa muhawarar da kalaman jarumar suka haifar na ci gaba da ɗaukar hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta a sassa daban-daban na ƙasar nan.
