
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamati na musamman da zai karbi bukatar duk wani ma’aikacin yada labarai dake san komawa makaranta danci gaba da karatu.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a lokacin da yake raba shaidar kammala horo na musamman na makonni shida da ma’aikatar ta baiwa ma’aikatan ta kan na’urar kwamfuta dan tafiya da zamani.
Ya kuma ce daga cikin abubuwan da ma’aikatar ta sanya a gaba harda baiwa ma’aikatan ta horo na musamman da kuma bawa kowane ma’aikaci damar ganin kwamishin kai tsaye musamman kananun ma’aikata don tafiya da aiki da kuma tattauna ci gaban ayyukan ma’aikatar yada labaran da bunkasa ayyukan ta.
Kwamared Waiya ya kuma ce dukkan wani ma’aikacin yada labarai yana da kyau ya iya sarrafa harshen sa zuwa harsunan da ake amfani dasu a guraren taruka daban-daban dan fitar da gwamnati da al’ummar Kano kunya.
Musamman Kwamishinan ya bawa ma’aikatan yada labaran shawarwarin tattaunawa yayin hira a ofishinsu da harshen turanci domin su kara gogewa da harshen don ci gaban su da kuma aikin su.
Yayin taron bayar da shaidar takardun kammala horon n makonni shida wanda kamfanin MiK-InforTech ya bayar ga ma’aikatan yada labaran na a karkashin ma’aikatar kwamishinan ya bayar da kyautukan kwamfuta ga kowane mutum daya cikin mutane uku da suka nuna hazaka a lokacin rubuta jarabawa ta musamman bayan kammala bada horon.
