
Hukumar Kula da Man Fetur ta kasa ta ce yawan man da ake hakowa a Najeriya zai iya kaiwa ganga miliyan 1.9 a kowace rana nan da wani lokaci bayan an samu ci gaba a fannin fitar da shi kwanan nan.
Babban Jami’in Hukumar na NUPRC, Oritsemeyiwa Eyesan ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wata ganawa da Shugaban Hukumar tattara Haraji ta Najeriya, Zacch Adedeji, a hedikwatar NRS da ke Abuja.
Kano first

Wannan dai na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Shugaban fitar a ranar Laraba.
Eyesan ya ce masana’antar mai ta kasarnan ta ci gaba da samun ƙaruwar samar da mai, yana mai lura da cewa yawan man da ake fitarwa ya kai ganga miliyan 1.86 a kowace rana a watan Mayu, wanda hakan ya sanya masana’antar a kan turbar murmurewa.
