
Daga Said Adam Muhammad
Masanin Harkokin Siyasa, Kano Najeriya
Yayin da tattaunawar siyasar zaben gwamnan Kano na shekarar 2027 ke kara daukar zafi, al’amuran cikin gida da suka dabaibaye tafiyar Kwankwasiyya na shiga wani mawuyacin yanayi mai cike da sarkakiya fiye da kowane lokaci a tarihin tafiyar.
Abin da ke faruwa yanzu ya wuce batun fitar da dan takarar gwamna kawai. A hankali lamarin na rikidewa zuwa wata babbar fafatawar siyasa da ta shafi aminci, gadon jagoranci, tasiri, da kuma makomar dorewar tsarin siyasar Kwankwasiyya gaba daya.
Tsawon shekaru, tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya assasa ta kasance daya daga cikin manyan tsare-tsaren siyasa mafi karfi a Arewacin Najeriya. Karfin tafiyar ya samo asali ne daga biyayya, jajircewar magoya baya, kyakkyawan tsari, da kuma yadda mabiyanta ke kallon tafiyar a matsayin akida, ba siyasa ta yau da kullum ba.
Sai dai duk wata tafiya mai karfi kan kai lokacin da tambayoyi game da gadon jagoranci da iko a cikin gida suke tasowa. A yanzu dai alamu na nuna cewa Kwankwasiyya ta kai wannan mataki.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, na daga cikin fitattun mutane masu cikakkiyar biyayya ga tafiyar. Yadda ya hakura da wani matsayinsa na siyasa domin komawa gaba daya cikin tafiyar Kwankwasiyya, mutane da dama sun dauki hakan a matsayin babbar sadaukarwa domin kare akida da tsarin tafiyar.
A wajen magoya baya da dama, irin wadannan sadaukarwa su ne ginshikin da aka gina Kwankwasiyya a kai. Saboda haka ne wasu ke ganin cewa shekaru na biyayya, gwagwarmaya, da jajircewa ya kamata daga bisani su haifar da sakamako a siyasance. Wannan ne ya sa batun magajin tafiyar ke kara tayar da hankali da motsin rai a tsakanin magoya bayan kasa.
A gefe guda kuma, Nasiru Yusuf Gawuna na ci gaba da bayyana a matsayin daya daga cikin manyan jiga-jigan siyasa a Kano a yau. Sakamakon da ya bayyana a zaben gwamnan da ya gabata ya tabbatar da cewa bai dogara da jam’iyya kadai ba, yana da karfin siyasa da farin jini musamman a cikin birnin Kano.
Sai dai kuma, wannan karfi nasa na iya zama babban abin damuwa ga wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a tafiyar Kwankwasiyya.
Ana kallon Gawuna ba kawai a matsayin dan takarar da zai iya lashe zabe ba, har ma a matsayin wanda zai iya zama mai cin gashin kansa idan ya hau mulki. A tarihi, ana ganin Kwankwaso mutum ne mai matukar kula da tasirinsa na siyasa, kuma baya son duk wata gwamnati da aka samar karkashin tafiyarsa ta kauce daga tasirinsa.
Wannan fahimta ce da ka iya zama babban kalubalen siyasar Gawuna duk da irin karfin da yake da shi wajen neman kuri’u.
A bangare guda kuma, akwai masu ganin cewa hana Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo tikitin gwamna na iya haifar da babban kalubale a cikin tafiyar. A wajen masu biyayya, nuna fifiko ga wadanda ake ganin sun zo daga baya ko kuma basu yi irin sadaukarwar da ya yi ba, na iya raunana kwarin gwiwar magoya bayan da suka kwashe shekaru suna kare tare da gina tafiyar.
Sai dai shi ma Abdussalam din na da nasa kalubalen siyasar.
Wasu masu nazarin siyasa na ganin halayensa na siyasa suna dauke da tsayin-daka da rashin son shiga karkashin ikon wani. Har ma wasu ke hasashen cewa idan har ya zama gwamna, akwai yiwuwar ya fi karfin duk wani tasiri daga waje fiye da yadda ake gani a gwamnatin Abba Kabir Yusuf a yanzu.
Wannan ne ke nuna cewa Kwankwaso na fuskantar wata irin matsin lambar siyasa daga kowanne bangare.
Idan ya mara wa mutum mai karfi kamar Gawuna baya, akwai yiwuwar daga baya ya samar da wani sabon karfi a siyasa da zai iya kalubalantar ikon tafiyar. Idan kuma ya goyi bayan mutum mai biyayya kamar Abdussalam, akwai yiwuwar shi ma daga baya ya zama wani jagora mai cin gashin kansa wanda ba zai amince da tasirin wani ba bayan ya hau mulki.
A lokaci guda kuma, akwai wata muhimmiyar gaskiyar siyasa da wasu masu sharhi suke watsi da ita, wato karfin Gwamna Abba Kabir Yusuf da yake ci gaba da kasancewa a tsakanin jama’a. Duk da sabanin siyasa da rikice-rikicen cikin gida, Abba na da dimbin goyon baya da soyayya daga talakawa a fadin Kano.
Kasancewarsa gwamna mai ci kuma na kara masa anfani ta fuskar iko, gani a idon jama’a, da kuma biyayyar wani bangare mai yawa na magoya bayan Kwankwasiyya. Saboda haka, kawar da shi daga siyasa ba abu ne mai sauki ba duk da irin lissafin da ake yi a bayan fage.
Wannan ne ya sa masu lura da al’amuran siyasa suka fara tambayar kansu ainihin alkiblar da siyasar cikin gida ta Kwankwasiyya ke dauka.
Shin rikicin da ake gani a yanzu wani bangare ne na dabarar siyasa domin kara karfafa tafiyar zuwa 2027? Ko kuwa a hankali yana rikidewa ne zuwa wata hanya da za ta iya raunana tare da raba kan tsarin da Kwankwaso ya kwashe shekaru yana ginawa?
Duk matakin da shugabancin Kwankwasiyya zai dauka yanzu yana dauke da manyan illolin siyasa. Kuskuren lissafi na iya haddasa rabuwar kai, raunana biyayya a tsakanin magoya baya, lalata martabar siyasar Kwankwaso, har ma da jefa daya daga cikin manyan tafiyoyin siyasa na Arewacin Najeriya cikin barazanar rarrabuwar kai.
Saboda haka watanni masu zuwa ba kawai za su tantance makomar wasu ‘yan siyasa ba ne, za su kuma iya zama masu yanke hukunci kan dorewa da hadin kan tafiyar Kwankwasiyya gaba daya.
