
Tsohon Ministan Harkokin Waje a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Yusuf Tuggar ya rasa tikitin takarar gwamnan Jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa Tuggar, wanda ya sauka daga mukaminsa na minista domin mayar da hankali wajen neman takarar gwamnan jihar, bai samu nasarar lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar ba.
An ce zaben fidda gwanin ya gudana cikin hamayya mai zafi tsakanin ’yan takarar da suka nemi wakiltar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar mai zuwa.
Magoya bayan tsohon ministan sun bayyana takaicinsu kan sakamakon zaben, yayin da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar suka bukaci mabiyansu da su rungumi sakamakon cikin lumana tare da hada kai domin ci gaban jam’iyyar.
Sai dai har zuwa yanzu, jam’iyyar APC a jihar Bauchi ba ta fitar da cikakken bayani kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin ba.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin rashin nasarar Tuggar na iya sauya yanayin siyasar jam’iyyar APC a jihar gabanin babban zaben shekarar 2027.
