
By Mutawakkilu Ibrahim Idris
Wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, kan zargin barazana ga tsaron ƙasa da ake yi masa.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da belin inda ta sanya kuɗin beli Naira miliyan 100
Kotun ta kuma gindaya sharadin cewa wanda zai tsaya wa El-Rufai dole ne ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro da ke Abuja.
Rahotanni sun ce ana tuhumar tsohon gwamnan ne kan wasu zarge-zarge da suka shafi tsaro, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da mabiyansa.
