
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya karɓi baƙuncin shugabannin da mambobin ƙungiyar ABBA GARO MANUFA ƊAYA, wadda ta bayyana aniyar ta na yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ya bayyana cikakken goyon bayan ƙungiyar ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da yin alƙawarin bayar da gudunmawa wajen ganin sun samu nasara a zaɓen 2027.
Shugaban ƙungiyar ya ce kowane mamba daga cikin mambobin ƙungiyar, wadda ke da sama da mambobi 2,000, ya ɗauki alƙawarin jawo aƙalla mutum goma domin su mara wa jam’iyyar APC baya daga sama har ƙasa.
Ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen ƙungiyar na ƙara faɗaɗa goyon bayan jam’iyyar APC a matakin ƙasa, jiha da ƙananan hukumomi.
A yayin ziyarar, ƙungiyar ta kuma ayyana Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya a matsayin Uban Ƙungiyar, tana mai bayyana amincewarta da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen hulɗa da jama’a da wayar da kan al’umma.
Da yake mayar da jawabi, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar bisa wannan ziyara da kuma ƙoƙarinsu na ƙarfafa haɗin kai tsakanin matasa da masu ruwa da tsaki a siyasa.
Kwamared Waiya ya yi kira ga shugabannin ƙungiyar da su ƙara jajircewa wajen wayar da kan al’ummar Jihar Kano kan muhimmancin zaɓen shugabannin da za su ci gaba da ayyukan raya jihar da samar da ci gaba.
Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da yin kira ga al’umma da su mara wa jam’iyyar APC baya daga sama har ƙasa, domin ci gaba da ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa.
Kwamared Waiya ya kuma yabawa shugabannin ƙungiyar bisa zaɓar sunan ABBA GARO MANUFA ƊAYA, yana mai cewa sunan na nuna manufar haɗin kai da mayar da hankali wajen cimma burin da ƙungiyar ta sanya a gaba.
A ƙarshe, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya karɓi matsayin Uban Ƙungiyar ABBA GARO MANUFA ƊAYA, tare da bayyana aniyarsa ta bayar da duk wata gudunmawar da ta dace wajen ganin ƙungiyar ta cimma manufofinta.
