By Mutawakkilu Ibrahim Idris
Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta bayar da beli ga wasu jami’an Gwamnatin Jihar Kano bayan wata takardar korafi da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya gabatar, kan zargin cin zarafi ta yanar gizo da kuma bata masa suna a kafafen sada zumunta.
DSS ta gayyaci jami’an tare da tsare su, inda ta yi musu tambayoyi na kusan sa’o’i hudu kafin daga bisani ta sake su bisa amincewar kansu (self-recognition).
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sunusi Bature Dawakin Tofa, Darakta Janar na Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnati Kano; Ibrahim Adam, Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai; Salisu Yahaya Hotoro, Shugaban Matasan APC a Kano; da Nuhu Dambazau, Babban Mai Ba da Rahoto na Musamman a Gidan Gwamnati.
Lamarin ya biyo bayan wata takardar ƙorafi da Sanata Kwankwaso ya miƙa ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya, inda ya zargi jami’an da amfani da kafafen sada zumunta wajen muzanta shi da wasu mambobin ƙungiyarsa ta siyasa.
A cikin ƙorafin mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Afrilu, 2026, Kwankwaso ya yi zargin cewa jami’an sun shiga cikin shirye-shiryen haɗin gwiwa a yanar gizo domin ɓata masa suna.
Sai dai, sakin jami’an bayan ɗan gajeren bincike da aka yi musu ya sa masu sa ido ke ganin cewa har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin, ba tare da an kai ga wata ƙarshe a kansu ba.
Wannan ci gaba ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara ta siyasa a kafafen sada zumunta tsakanin magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da kuma masu goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga DSS ko Gwamnatin Jihar Kano kan lamarin.
