
Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar jama’a sama da mutum 500 ta hanyar amfani da wayar tarho, inda suke kwaikwayon “aljannu” domin tsoratar da mutane su tura kuɗi.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 10 ga Afrilu, 2026, sakamakon sahihan bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu.
Wadanda ake zargin sun haɗa da Ahmad Ibrahim mai shekaru 24 da kuma Isma’il Muhammad mai shekaru 22, dukkansu mazauna unguwar Dandinshe da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano.
Binciken ’yan sanda ya nuna cewa matasan na amfani da fasahar sauya murya wajen kiran mutane, inda suke gabatar da kansu a matsayin “aljannu”, tare da tsoratar da su da barazanar kamuwa da cuta ko wata matsala ta ruhaniya idan ba su bi umarninsu ba.
A cewar rundunar, matasan kan umarci waɗanda suka kira da su aikata wasu abubuwa, ciki har da tura kuɗi, tare da yi musu barazana da mummunan sakamako idan suka ƙi.
’Yan sandan sun kuma bayyana cewa waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin, inda suka damfari mutane sama da 500 tare da karɓar kuɗaɗe da wasu kayayyaki daga hannunsu.
Haka kuma, rundunar ta ce ta ƙwato katin layi (SIM) guda 28 da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan, yayin da bincike ke ci gaba domin gano sauran waɗanda ke da hannu a cikin wannan haramtacciyar ƙungiya.
Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da bincike tare da tabbatar da gurfanar da duk masu hannu a cikin lamarin a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa doka.
