
Kano Facebook Connect 2026: Gwamnati Ta Jaddada aniyarta na Tallafawa Matasa – Waiya. By Mutawakkilu
Kwamishinan Yaɗa Labarai da al’amuran cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da ƙudurin tallafawa da bunƙasa cigaban matasa domin su bada gudummawa ga ci gaban jihar.
Ya faɗi haka ne a taron Kano Facebook Connect 2026, inda ya bayyana taron a matsayin wata muhimmiyar dama ga matasa wajen haɗin gwiwa da ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar fasahar zamani.
Waiya ya buƙaci matasa su juya ilimi da alaƙar da suka samu daga taron zuwa ayyuka masu amfani ga al’umma, yana mai jaddada cewa gwamnati a shirye take ta tallafa musu.