By Khadijah Shehu Abdulkareem

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana Juma’a, 5 ga Satumba, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W).
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar a ranar Laraba, wadda babbar sakatariya a ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
A duk shekara, miliyoyin Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya kan gudanar da bukukuwan Maulidi, domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).
Gwamnatin ta yi kira ga al’ummar ƙasa da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i na samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da haɗin kai, musamman ganin irin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar.
