
Taron wanda ya gudana a dakin taron dake headquarter Yan sanda ta jihar kano dake bamfai a karkashin shirin (SAFE CORRIDOR PROJECT) Wanda gwamnatin Kano ta samar domin magance fadace fadacen daba.
Taron yasamu bakunchin manyan Jami,an tsaro daga sassa daban daban ciki harda shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Jihar Kano ACGN Ahmad Idris Abubakar, da babban malamin addinin musulunci sheikh Aminu Ibrahim daurawa
A yayin taron Malam daurawa yaja hankalinsu da su tuba ga Allah Sannan su kiyayi duk abinda zai taba martabarsu da ta Yan uwansu.
Shima anashi bangaren Kwamishinan Yan sanda na Jihar Kano CP Ibrahim Adamu bakori Ya tabbatarwa da wadannan tubabbun Yan Daban cewa hukumarsu zatayi duk Mai yuwuwa wajen temaka musu domin su zama chikakkun mutane na gari.
Anashin bangaren, wakilin mai martaba Sarkin kano Malam Muhammadu sunusi II Alh shehu Muhammad Dankade Ya godewa gwamnatin Kano bisa kokari da take wajen magance matsalolin tsaro a fadin Jihar, Sannan ya ja hankalin wadannan matasa dasu kauracewa fadace fadacen daba a tsakaninsu
Akarshe kwamishinan yada labarai ya Kara tabbatarwa da wadannan matasa cewa gwamnati zatayi duk Mai yuwuwa wajen ganin ta inganta rayuwasu.
Signed
Mutawakkilu Ibrahim
20 August 2025
